Sojojin Juyin Mulkin Gabon Sun Cafke Dan Shugaba Ali Bongo

Sojojin Juyin Mulkin Gabon Sun Cafke Dan Shugaba Ali Bongo

  • Sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo a ƙasar Gabon a ranar Laraba, sun bayyana cewa hamɓararren shugaban yana tsare a gidansa
  • Sojojin sun kuma cafke ɗan hamɓararren shugaban ƙasar da wasu ƙusoshin gwamnati bisa zargin aikata laifin cin amanar ƙasa
  • Sojojin sun kuma soke zaɓen shugaban ƙasar da aka yi kwanan nan, wanda aka sake zaɓen Ali Bongo a matsayin shugaban ƙasa karo na uku

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Libreville,Gabon - An cafke ɗaya daga cikin ƴaƴan hamɓararren shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo Ondimba, bisa zargin cin amanar ƙasa.

Hamɓararren shugaban ƙasar kuma an killace shi a gidansa tare da wasu daga cikin iyalansa, cewar rahoton France 24.

Sojoji sun cafke dan Shugaba Ali Bongo
Sojoji sun cafke dan hambararren Shugaba Ali Bongo na Gabon
Asali: Getty Images
"Shugaba Ali Bongo yana tsare a gidansa, tare da shi akwai iyalansa da likitoci." A cewar sojojin

Sojojin dai sun kifar da gwamnatin Bongo ne da safiyar ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, inda suna soke zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar na ranar Asabar wanda Bongo ya lashe.

Kara karanta wannan

Muhimmin Abubuwa 5 Dangane Da Shugaban Sojojin Da Suka Kifar Da Gwamnati a Gabon

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar hukumar zaɓen ƙasar, Shugaba Ali Bongo ya lashe kaso biyu bisa uku na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen na ranar Asabar.

Sojojin sun sanar da cewa sun rushe dukkanin ma'aikatun gwamnatin ƙasar, majalisar dokoki da kulle iyakokin ƙasar. Sun bayyana cewa sun yi hakan ne a madadin dakarun tsaron ƙasar.

Dalilin cafke ɗan Ali Bongo

Ɗan Bongo da mashawarcinsa na kusa, shugaban ma'aikatansa, Ian Ghislain Ngoulou, tare da mataimakinsa, wasu mutum biyu masu ba shugaban ƙasa shawara da wasu manyan jiga-jigai mutum biyu na jam'iyya mai mulki ta Gabonese Democratic Party (PDG), an cafke su.

Wani jagoran sojoji ya bayyana cewa ana zarginsu ne da cin amanar ƙasa, almubazzaranci, cin hanci da yin sa hannun shugaban ƙasar na ƙarya da wasu zarge-zargen.

An Kifar Da Gwamnatin Ali Bongo

Kara karanta wannan

Bidiyon Halin da Hamɓararren Shugaban Ƙasar Gabon Ke Ciki Ya Bayyana, Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci

A baya rahoto ya zo cewa sojoji a ƙasar Gabon da ke yankin Afirika ta Tsakiya, sun sanar da kifar da gwamnatin farar hula a ƙasar.

Sojojin da suka yi juyin mulkin sun sanar da cewa sun hamɓarar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo, wanda ya hau karagar mulkin ƙasar a shekarar 2009.

Asali: Legit.ng

Online view pixel