Wani Faifan Bidiyo Ya Nuna Yadda Aka Gudanar Da Ranar Mahaukata Ta Duniya A Kano

Wani Faifan Bidiyo Ya Nuna Yadda Aka Gudanar Da Ranar Mahaukata Ta Duniya A Kano

  • Yayin ake karkare bikin ranar Hausa ta duniya, an sake samun wata sabuwar ranar murna da ake cewa ranar mahaukata
  • Wannan rana an gudanar da bikin ne a yau Talata 29 ga watan Agusta a birnin Kano inda mutane ke shigar mahauka
  • An gano mutanen a cikin wani faifan bidiyo sanye da kazaman kaya wanda Zagazola Makama ya yada a shafin Twitter

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Wata sabuwar rana ta samu a jihar Kano bayan an gano wasu matasa na bikin ranar mahaukata ta duniya.

A cikin wani faifan bidiyo an gano lokacin da wasu gungun mutane sanye da tsummokara ke fareti a kan tituna.

An gudanar da bikin ranar mahaukata a Kano yayin da aka kammala ranar Hausa
Masu Gudanar Da Bikin Ranar Mahaukata Ta Duniya A Kano. Hoto: @ZagazOlaMakama.
Asali: Twitter

Wane biki 'yan Kano ke yi?

A cewar wani sakon Twitter da Zagazola ya wallafa ranar Talata 29 ga watan Agusta, an gudanar da taron ne a birnin Kano.

Kara karanta wannan

Yadda Likitoci Suka Gano Tana Mai Rai A Kwakwalwar Wata Mata

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake yada bidiyon, ZagazOlaMakama ya rubuta kamar haka:

“Yau a Kano, an gudanar da bikin ranar mahaukata ta duniya.”

A cikin faifan bidiyon an jiyo wani yana magana cikin harshen Hausa da cewa:

"A rayuwa babu abin da ba za ka gani ba, yau kuma ga sarkin mahaukata ta duniya.
"Yau ranar mahaukata ce ta duniya, ga wasu can sun kwanta shan kwata a ranar mahaukata ta duniya.
"To ga kasurgumin babban mahaukacin nan, shugaban mahaukatan duniya, hauka ga mai kare ka."

Wannan na zuwa ne bayan an kammala bikin ranar Hausa ta duniya wanda aka yi a ranar Asabar 26 ga watan Agusta, kamar yadda Punch ta tattaro.

Kamar yadda aka sani dai Kano na daga cikin garuruwa da Hausawa ke rayuwa a Arewacin Najeriya.

Garin Kwaki Ya Yi Ajalin Yarinya Tare Da Galabaita Wasu 5 A Kano

Kara karanta wannan

Jan aiki: Sojojin Najeriya sun lalata wata matatun mai da ake aiki ba bisa ka'ida ba

A wani labarin, yayin da ake ci gaba da fuskantar matsin rayuwa a Najeriya, masifa ta afkawa wasu iyali a jihar Kano inda ake zargin garin kwaki ya yi ajalin wata yarinya.

Rahotanni sun tabbatar cewa yarinyar mai suna Firdausi Mahmud Abdullahi ta kwanta dama sakamakon cin garin kwaki da ta yi.

Wannan na zuwa ne bayan ta shafe tsawon lokaci ba tare da ta saka komai a cikinta ba, wanda hakan ya kuma galabaitadda sauran 'yan uwanta su guda biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel