Kaduna: Zaki ya kufce daga gidan ajiyan namun daji dake cikin filin shakatawa na Gamji

Kaduna: Zaki ya kufce daga gidan ajiyan namun daji dake cikin filin shakatawa na Gamji

- Mutane sun shiga rundani a filin shakatawa na Gamji dake jihar Kaduna yayin da zaki ya kufce daga cikin dakin ajiyan sa a ranar Asabar

- Zaki ya kubce a filin gamji yayin da mai kulawa da shi yake bashi a abinci

A ranar Asabar mutanen dake zuwa shakatawa a Gamji Gate suka tsallake rijiya da baya yayin da wani zaki ya kufce daga dakin da ake ajiye shi.

Legit.ng ta samu rahoton cewa zakin ya kufce ne yayin da daya daga cikin masu kula da shi ke bashi abinci.

Rahotannin sun nuna zakin cewa yayi ragaraga da wanda yake kula da shi kafin ya samu nasarara ficewa daga dakin da aka ajiye shi.

Kaduna: Zaki ya kufce daga gidan ajiyan namun daji dake cikin filin shakatawa na Gamji
Kaduna: Zaki ya kufce daga gidan ajiyan namun daji dake cikin filin shakatawa na Gamji

An yi ta gudu a filin Gamji bayan da masu shakatawa su ka tsinkayi Zakin.

KU KARANTA : Jerin muhimman kalmomin hausa 20 da ma'anar su a harshen turanci

Wadanda suka shaida lamarin da idonsu sun fadawa manema labaru cewa zakin da kan sa ya koma cikin inda aka killace shi ba tare da ya kassara wani mutum ba.

Filin shakatawa na Gamji a Kaduna na da karamin wurin ajiye namun daji wato, Zoo kuma akwai Zaki, da Jimina, da wasu Birai, Bareyi da kuma Kuraye.

Akan zargi masu killace irin wadannan namun daji da barin su cikin yunwa, abinda watakila ya sa su ke tunzura har su yi kokarin kufcewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: