Zaki ya cinye wadansu mafarauta dake kisan cin zali ga namun daji
- An haramta farauta ba bisa ka'ida ba dama a gandun dazukan duniya
- MAfarautan kan yi kisan gilla kan dabbobi don neman kudi
- Sukan ciri haure da sauran sassan jiki don sayarwa a kasuwannin duniya
Mafarautan Karkanda a dazuka domin su cire masa qaho da gabbai sun shiga hannun sarkin dawa inda yayi musu hukunci dai-dai da laifukansu ga namun daji bayin Allah da ake cimma zali ba da al-hakinsu ba.
Zakunan dai, sun cinye mafarautan ne yayin da suke aikin sunquru da dauki dai-dai kan namun dajin da dama sun yi kasa a gandun dajin na Afirka ta kudu.
Da yawa daga dabbobin da mafarautan kan kashe tuni dama an sanya su cikin wadanda ake tsoron zasu kare a duniya muddin ba'a daina farautarsu ba.
DUBA WANNAN: An kamo wadanda suka yankwana lauya a bidiyo
Jami'ai masu kula da namun daji ne suka gano ragowar gawawwakinsu wadanda ake kyautata zaton na mutum biyu ko uku ne a wani wuri da zaki yake da iko a wurin kula da namun daji na Sibuya da ke kusa da garin Kenton.
An kuma gano wata babbar bindiga da aka tsinta a kusa da wurin.
Karkanda dai shine Rhino a turance, wanda yara kan ce wa mugun-dawa.
Ana samun karuwa yawan masu fataucin namun daji a nahiyar Afirka shekarun baya-baya nan saboda yawan bukatar da ake yiwa kahon karkanda a wasu sassan nahiyar Asiya.
Kasashen China da Vietnam da sauran wurare, sun yi amannar cewa za'a iya yin amfani da kahon karkandar wajen yin magani.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng