Mace ta kori zaki da kara don kar ya cinye mata akuyarta
- Zaki a da baya tsoron mutane, amma yanzu sukan fatattake shi saboda ana yawan farautarsa
- Raguwar dazuka ta sanya ake hadewa tsakanin dabbobin dawa da na gida
- Matar ta kori zakin ta ceci akuyarta a kauye
Wata budurwa a kasar Indiya, ta tsallake rijiya da baya nayan da ta far ma zaki da sanda waidon ta ceci akuyarta da ya kawowa hari domin farauta.
Rupali Meshram, 'yar shekara 23 da haihuwa, ta ce bayan da ta ji akuyar ta na ihu, sai ta yi maza ta ruga ta nufi inda akuyar ta ke a wajen gidansu.
DUBA WANNAN: Saudiyya ta canja salon siyasar ta kan Israila
Daga nan ne sai ta dauki sanda ta fara dukan zakin, wanda daga baya kuma ya afka mata. Mahaifiyarta wadda ita ma ta samu raunuka, ita ta cece ta ta hanyar ingizata cikin gida.
Ana yawan samun irin wadannan hare-hare a kauyukan Indiya, saboda kusanci da suke da shi da dazuka, yawan al'umma, zaman karkara, da ma kuma karuwar yunwa tsakanin dabbobin dawa.
A duniya dai, saboda yawan hari da farauta da ake yi wa zakuna, suna fuskantar barazana daga bacewa a doron duniya abin da ake kira extinction, wanda hakan ba zai yi wa dunia ko dabbobin daji dadi ba.
Ba wai don zaki shiine sarkin dawa ba, a'a, sai don arautar tasu tana taimakawa na rage yawan dabbobin da ma kuma zaburar da su su rika motsa jiki, da ma kuma kyaun tsarin tsani/matakin abinci wanda ake kira food-chain.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng