Gwamnatin Tarayya Ta Ba Tsohon Shugaban EFCC Bawa Damar Ganin Lauyoyi Da Yan Uwansa

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Tsohon Shugaban EFCC Bawa Damar Ganin Lauyoyi Da Yan Uwansa

  • Gwamnatin tarayya ta yi umurnin ba Abdulrasheed Bawa, dakataccen shugaban hukumar EFCC damar ganin lauyoyi da yan uwansa
  • An tattaro cewa Bawa ya ki bai wa masu bincikensa hadin kai ta hanyar amsa tambayoyi da ake masa
  • Tawagar lauyoyinsa sun ki shigar da kara kotu don neman a sake shi saboda umurnin da mahaifinsa ya bayar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gwamnatin tarayya ta yi umurnin cewa a bai wa dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, damar ganin lauyoyi da yan uwansa.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa lauyoyi da yan uwansa na ganinsa a inda yake tsare a hannun hukumar tsaron farin kaya na tsawon makonni yanzu.

Abdulrasheed Bawa
Gwamnatin Tarayya Ta Ba Tsohon Shugaban EFCC Bawa Damar Ganin Lauya Da Yan Uwansa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Bawa ya ki bai wa masu bincike hadin kai

An tattaro cewa kalubalen da ake fuskanta shine ya ki ba masu bincike hadin kai ta hanyar amsa masu tambayoyi da jawabai kamar yadda ake bukata.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kwastomomi Sun Rage Zuwa Gida Karuwai a Kano, Gidan Magajiya Ya Dauki Zafi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:

"Matashin ya ki ba masu bincike hadin kai. Ya ki amsa tambayoyi. Ya kuma ki yin jawabi. Mun fahimci cewa hakan na cikin hakkinsa na yin jawabi da kansa ko ya ki. Ina ganin a yanzu ana duddubawa don ganin mataki na gaba da za a dauka."

Mahaifin Bawa ya hana mu neman a sako shi, Lauya

Hakazalika, wani babban lauya, wanda ya zanta da jaridar The Nation a sirri, ya ce an hana tawagar lauyoyin Bawa nema masa yanci a kotu saboda umurnin da mahaifinsa ya bayar.

“Da yanzu mun shigar da kara na tabbatar da yancinsa. Za ku tuna cewa matashin ya shafe watanni a tsare, inda gwamnati ta ki gurfanar da shi a kotu.
"Mun zama babu yadda za mu yi ne saboda umurnin mahaifinsa wanda ya bukace mu da kada mu je kotu a madadinsa.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Kwanaki kadan da yin ritaya, tsohon kakakin soja ya kwanta dama

"Mahaifin nasa ya ce ya yarda za a saki dansa a lokacin da Allah ya nufa kuma cewa babu bukatar maka gwamnati kara a kotu."

Lauyoyi sun nemi gwamnatin Tinubu ta saki Bawa

A halin da ake ciki, wasu manyan lauyoyin Najeriya na ci gaba da neman a saki Bawa, inda Rotimi Jacobs ne ya yi kiran a baya-bayan nan.

Jacobs ya bayyana ci gaba da tsare Bawa da ake yi tun daga ranar 14 ga watan Yuni a matsayin wanda baya bisa doka, rahoton Channels TV.

A wata sanarwa da ya fitar, ya yi misali da tanadin dokar ACJA na 2015 dangane da ikon da kasa ke da shi na tsare wanda ake zargi, sannan ya yi korafin cewa dokar tsare mutum ya nuna cewa tsare Bawa da ake yi a yanzu bai da wani hujja a shari'a.

Jacobs ya ce adadin kwanakin tsare wanda ake zargi a Najeriya shine kwana 56, yana mai cewa an tsare Bawa fiye da yadda doka ta tanada, wanda kuma ya saba wa doka, kuma dole ne dukkan masoyan dimokradiyya su yi adawa da shi.

Kara karanta wannan

“Budurwarsa Ta Ba Shi Kunya”: Malamin Addini Ya Yi Tsalle Daga Ginin Bene Mai Hawa 2, Ya Mutu a Anambra

Wasu Manyan Lauyoyi guda biyu, Femi Falana da Kemi Pinheiro suma sun gabatar da irin wannan muhawarar wajen neman a saki Bawa.

Babu dokar da ta hana mai NYSC zama minista, Hannatu Musawa

A wani labari na daban, mun ji cewa Hannatu Musawa, Minsitan Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira, ta magantu kan dambarwar cewa an nada ta minista kasancewa a halin yanzu ita yar yi wa kasa hidima ne wato NYSC.

Kungiyar Marubuta Masu Kare Hakkin Bil Adama, HURIWA, ne ta fara janyo hankalin mutane kan cewa Musawa yar yi wa kasa hidima ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel