Abdulrasheed Bawa: Majiya Ta Ce Rawar Da Ya Taka Kan Fasalin Sauya Naira Yasa Ake Tsare Da Shi

Abdulrasheed Bawa: Majiya Ta Ce Rawar Da Ya Taka Kan Fasalin Sauya Naira Yasa Ake Tsare Da Shi

  • Mako guda bayan dakatar da shi, har yanzu tsohon shugaban hukumar Yaƙi Da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa na hannun jami'an DSS a Abuja
  • Ana tsare da Bawa ne tare da Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN)
  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dakatar da Bawa da Emefiele daga ayyukansu bisa zargin cin zarafin ofisoshinsu

FCT, Abuja - Har yanzu Abdulrasheed Bawa, dakataccen shugaban Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), na hannun hukumar DSS.

Har yanzu ana ci gaba da tsare Bawa mako guda bayan dakatar da shi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuni.

Har yanzu Bawa na tsare a hannun DSS
Har yanzu jami'an DSS ba su kammala bincike ba akan Bawa. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Ana tuhumar Bawa bisa rawar da ya taka kan sake fasalin naira

Kara karanta wannan

Halin Da Dakataccen Shugaban EFCC Yake Ciki Sati Daya Bayan DSS Ta Yi Caraf Da Shi

Duk da cewa jami’an ‘yan sandan na farin kaya ba su bayyana laifinsa ba, majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da tuhumar Bawa ne a kan rawar da ya taka kan batun sake fasalin naira a gwamnatin da ta shuɗe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyar ta ce ko da yake akwai wasu batutuwan da ake tuhumarsa da su na daban, rawar da ya taka kan ƙarancin kuɗi a watan Fabrairu ce kan gaba a cikin laifukan nasa.

Idan dai za a iya tunawa, kwanaki 16 bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa kuma bayan ganawar da ya yi da Bawa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban na EFCC. Daga nan kuma DSS suka yi ran da shi.

Jami'an DSS sun farmaki gidan Bawa don gudanar da bincike

Kara karanta wannan

Ciki Ya Ɗuri Ruwa, DSS Sun Je Gidan Abdulrasheed Bawa, An Zurfafa Binciken EFCC

A wani labarin da Legit.ng ta ruwaito, jami’an hukumar DSS sun kai farmaki gidan Abdulrasheed Bawa da ke Gwarinpa, Abuja a ranar Asabar, 17 ga watan Yuni. Sun gudanar da bincike a yayin da matarsa ​​da ‘ya’yansa ke ciki.

Jami’an na DSS sun kuma yi bincike a ofishin sa da ke hedikwatar EFCC tare da gayyatar makusantansa domin amsa tambayoyi.

Jam'iyyar Peter Obi ta nemi Tinubu ya dakatar da shugaban INEC

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto na jam'iyyar Labour da ta ce ba ta ji daɗin dakatarwar da Shugaba Tinubu ya yi wa gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ba.

Jam'iyyar ta Labour ta ce kamata ya yi shugaban ƙasar ya dakatar da shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, sannan kuma ya sanya a bincikesa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel