Ganduje na kokarin tsige Rimingado saboda bincikar iyalansa da yake kan wasu kwangiloli
- An gano cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje na kokarin tsige shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar
- Wani dan majalisa a jihar Kano ya tabbatar da cewa Ganduje ya tsananta sai majalisa ta fatattaki Muhuyi Rimingado
- AN gano cewa hakan yana da alaka da binciken da Rimingado ya fara kan iyalan gwamnan kan wasu kwangiloli da aka basu
Jihar Kano
Kokarin tsige shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar Kano, PCAC, Muhuyi Rimingado, ya tsananta sakamakon zargin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ake na takurawa majalisar jihar kan aiwatar da hakan.
Wasu majiyoyi daga majalisar jihar sun sanar da Daily Nigerian cewa gwamnan yana so yayi amfani da 'yan majalisar wurin korar shugaban hukumar saboda katsalandan da yayi ga lamurran iyalansa.
KU KARANTA: Bidiyon saurayin da ya baiwa budurwa kyautar N2.5m saboda ta amince zata aure shi
KU KARANTA: Amurka: An yankewa dan sandan da ya kashe bakar fata Floyd shekaru 22.5 a gidan yari
Dan majalisar jihar Kano ya fallasa
"Akwai wani shiri da gwamna ke yi na tsige Muhuyi. Duk da gwamnan bai sanar da takamaiman laifin Muhuyi ba, yana dai so ne kawai ya tsige shi daga kujerarsa.
"Kun san gwamnan ya saba tirsasa 'yan majalisar jihar karbar aradu da kai, ko da kuwa shi lamarin ya shafa. Ku tuna yadda yayi har ya ga bayan mataimakinsa, Hafiz Abubakar da tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II," wani dan majalisa ya sanar da hakan.
A yuwuwar aukuwar shirin gwamnan, dan majalisar yace da yawa 'yan majalisar zaune suke kawai, kuma zasu bi bayan gwamnan, Daily Nigerian ta ruwaito.
Rimin Gado yana bincikar iyalan gwamna
Rikicin ya fara ne a farkon watan nan lokacin da Rimingado ya haskaka bincikensa kan wasu kwangiloli da ake zargin an baiwa kamfanoni masu alaka da iyalan gwamnan.
A wani labari na daban, kungiyar tsageru ta Niger Delta Avengers, wacce aka sani da tada kayar baya a yankin Niger Delta yayin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na farko, sun sanar da dawowarsu, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Idan za a tuna, kungiyar ta gurgunta tattalin arzikin Najeriya daga 2016 zuwa 2018 ta hanyar kai farmaki wuraren diban man fetur dake yankin, lamarin da yasa kasar Najeriya ta fada karayar tattalin arziki.
A wata takarda da suka baiwa manema labarai a ranar Asabar, kungiyar tsagerun ta ce ta kaddamar da 'Operation Humble' wanda take son amfani dashi wurin gurgunta tattalin arzikin kasar nan kamar yadda tayi a baya.
Asali: Legit.ng