“Budurwarsa Ta Ba Shi Kunya”: Malamin Addini Ya Yi Tsalle Daga Ginin Bene Mai Hawa 2, Ya Mutu a Anambra
- Wani fasto mai shekaru 30, Prosper Igboke, ya yi mutuwar bakin ciki ta hanyar fadowa daga ginin bene mai hawa biyu a yankin Nnewi, jihar Anambra
- An yi zargin cewa faston ya dauki matakin dira daga benen saboda budurwarsa da ya dauki nauyin karatunta har jami'a ta bada masa kasa a ido
- Yan uwan Igboke sun bayyana cewa saboda kashe kansa da ya yi, za a binne shi ne a cikin jeji kamar yadda yake bisa al'ada
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Nnewi, jihar Anambra - Rahotanni sun kawo cewa Fasto Prosper Igboke, mai shekaru 30 ya yi tsalle ya duro daga ginin bene mai hawa biyu a Nnewi, jihar Anambra.
Marigayin, wanda ya kasance fasto a cocin Pentecostal, ya yi tsalle daga ginin benen sakamakon kasa da budurwarsa ta bada masa a ido, jaridar The Nation ta rahoto.
Wani dan uwan marigayin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce budurwar ta ki amsa tayin aurensa bayan ya gama daukar dawainiyarta har ta gama jami'a.
"Lamarin ya faru ne a watan jiya. Ya kasance dan shekara 30 a lokacin da ya mutu. Budurwarsa, wacce ya yi niyar aura ta ba shi kunya bayan ya gama daukar dawainiyarta har zuwa jami'a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ya yi tsalle daga ginin bene mai hawa biyu sannan ya mutu. Na yi mamaki cewa mutuwan wannan shekaru kuma fasto zai iya yin wannan," inji dan uwan nasa.
Za a binne Prosper Igboke a dokan daji
A cewar dan uwan nasa, za a binne Igboke wanda ya kasance dan Umunneochi, jihar Abia a dokan daji saboda ya kashe kansa.
Ya ce:
"Za a binne shi a daji saboda kashe kansa kamar yadda yake bisa al'adar al'ummar Leru na karamar hukumar Umunneochi a jihar Abia.
"Kyau Iya Kyau": Bidiyon Jarumar Fim Da Biloniyan Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet
A cewar jaridar Nigerian Tribune, daga karshe an binne marigayin a wani daji da ke garinsu.
Amarya ta fadi ta mutu a ranar aurenta
A wani labari na daban, mun ji cewa wata amarya mai suna Rebecca Oyedotun, ta yanke ciki ta fadi matacciya a ranar aurenta a yankin Ogbomoso da ke jihar Oyo.
Mummunan al'amarin ya afku ne a jajiberin ranar aurenta yayin da ake bikin wankar amarya tare da kawayenta.
Asali: Legit.ng