Gwamna Inuwa Yahaya Ya Samu Nasarar Zama Shugaban Gwamnonin Arewa

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Samu Nasarar Zama Shugaban Gwamnonin Arewa

  • Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa NGF
  • Inuwa zai ɗora daga inda gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya aje a kujerar shugaban ƙungiyar
  • Ya ce zai yi iya bakin ƙokarinsa wajen tabbatar da ba'a bar yankin arewa a baya ba, kuma zai tabbatar al'umma sun amfaana

Gwamnan jihar Gombe da ke Arewa maso Gabas, Muhammad Inuwa Yahaya, ya yi nasarar zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya (NSGF).

Gwamna Yahaya, wanda ya hau gadon mulkin jihar Gombe a 2019, ya sake lashe zaben tazarce kan kujerarsa a babban zaben da ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Muhammad Inuwa Yahaya.
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Samu Nasarar Zama Shugaban Gwamnonin Arewa Hoto: Abu Ammar/Facebook
Asali: Facebook

A halin yanzu, Inuwa Yahaya ya gaji gwamnan jihar Filato mai barin gado, Simon Bako Lalong, a matsayin shugaban ƙunguyar NSGF, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Jiga-Jigan Jam'iyyun Adawa Da Tinubu Zai Naɗa Bayan Rantsarwa

Zamu yi iya bakin kokarin mu - Inuwa

A jawabin karban mukamin, Gwamna Inuwa Yahaya, ya sha alwashin cewa zai yi iya bakin kokarinsa wajen sauke nauyin da takwarorinsu suka ɗora masa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Inuwa, a wata sanarwa da darakta yaɗa labaransa, Isma'ila Misilli, ya fitar, ya ce:

"Zamu yi aiki tuƙuru don tabbatar da cewa arewa ta kamo sauran sassan ƙasar nan, idan ta yuwu ma mu yi gogayya da wasu sassan duniya da suka ci gaba domin al'ummarmu ta amfana da shugabanci na gari."

Ya ce Allah ya yi wa arewa ɗumbin arziƙi, ba wai ɗanyen mai da gas kaɗai ba, harda ma'adanan ƙasa wanda a ganinsa ba dalilin da zai hana NGF amfani da wannan dama domin talakawa su ji daɗi.

A nasa jawabin, gwamna Simon Lalong, ya buƙaci magajinsa ya yi amfani da basirar da Allah a ba shi a ɓangaren jagoranci ya sauke nauyin da ke kan shugaban NGF, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Fitaccen Farfesa a Arewacin Najeriya, Irinsa Na Farko a Nahiyar Afirika Ya Mutu

Gwamna Makinde Ya Rushe Majalisar Zartaswa

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Makinde Ya Rushe Majalisar Zartaswa, Ya Kori Hadimansa.

Gwamna Seyi Makinde ya rushe majalisar zartarwan jihar Oyo, ya umarci mambobi su sauka daga makamansu daga ranar 23 ga watan Mayu, 2023.

Gwamnan na ɗaya daga cikin gwamnonin jam'iyyar PDP da suka samu nasarar tazarce a babban zaɓen 2023.da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel