Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Yan Sanda a Jihar Delta, An Rasa Rai

Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Yan Sanda a Jihar Delta, An Rasa Rai

  • Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan daba ne sun farmaki hedkwatar 'yan sanda a ƙaramar hukumar Ethiope ta gabas a jihar Delta
  • Maharan sun halaka jami'in ɗan sanda guda ɗaya yayin wani ɗan sanda ke kwance a Asibiti ana kulawa da raunukan da ya samu
  • Jami'in hulɗa da jama'a na 'yan sandan Delta, DSP Bright Edafe, ya ce maharan ba su sace bindigar AK47 ta mamacin ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Delta - Rahotanni sun nuna cewa an bindige ɗan sanda ɗaya har lahira ranar Alhamis da daddare a garin Isiokolo, hedkwatar ƙaramar hukumar Ethiope ta gabas a jihar Delta.

Bayan halaka ɗan sanda, ƙarin wani jami'in ɗan sanda na kwance a Asibiti yana karɓan magani bayan wasu 'yan bindiga sun kai farmaki hedkwatar 'yan sanda da ke Isiokolo.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Yan bindiga sun kai hari hedkwatar yan sanda.
Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Yan Sanda a Jihar Delta, An Rasa Rai Hoto: Policeng
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wasu matasa a kan babura ɗauke da makamai ne suka mamayi Ofishin 'yan sandan, inda suka buɗe wa jami'an da ke bakin aiki wuta kan mai uwa da wabi.

Yayin haka ne 'yan bindigan da ake kyautata zaton 'yan daba ne suka yi ajalin ɗan sanda guda ɗaya nan take yayin da wani daban ya ji raunukan harbin bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin ga 'yan jarida.

Sai dai ya musanta rahoton da ke yawo cewa maharan sun kwace bindigar AK47 ta ɗan sandan da suka kashe.

Wane hali ake ciki a yanzu bayan wannan hari?

DSP Edafe ya ƙara da cewa a halin yanzu, jami'in ɗan sanda da ya samu rauni yana kwance a Asibiti ana masa magani.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

A kalamansa, kakakin 'yan sandan jihar Delta ya ce:

"Ba a sace bindigar ‘yan sanda a ofishin ba. An harbe wasu jami'ai da ke aiki a ofishin, ɗan sanda daya ya mutu, wani kuma yana asibiti ana masa magani."

Har kawo yanzu dai ba a bayyana ainihin dalilin da ya sa ‘yan bindigar suka afkawa ofishin ‘yan sandan ba, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Hukumar Yan Sanda Ta Musanta Ikirarin Ɗan Bindiga Ya Zama Gwamna a Neja

A wani bangaren Hukumar 'yan sanda ta ƙaryata rahoton da ke yawo cewa wani shugaban 'yan bindiga ya ayyana kansa a matsayin gwamnan Neja.

Kakakin 'yan sandan jihar, Wasi'u Abiodun, ya ce rahoton ƙanzon kurege ne kuma jami'an tsaro na aiki tukuru domin dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel