Sama Da Shekara 5 Muka Shafe Muna Satar Awaki, Barayin Dabobi Da Aka Kama a Neja

Sama Da Shekara 5 Muka Shafe Muna Satar Awaki, Barayin Dabobi Da Aka Kama a Neja

  • 'Yan sandan jihar Neja sun yi ram da wasu ƙwararrun ɓarayin dabbobi da suka addabi al'umma
  • An bayyana cewa ɓarayin sun shafe sama da shekara biyar suna ta'adi ba tare da an yi nasarar kama su ba
  • Da suke amsa tambayoyi, ɓarayin sun tabbatar da cewa sun sace sama da awaki 500 a wannan lokacin

Minna, jihar Neja - Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta yi nasarar kama wasu mutane huɗu da suka ƙware wajen satar dabbobi a cikin Minna babban birnin jihar.

Sun ce sun shafe aƙalla shekara biyar a harkar ta satar dabbobi kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

'Yan sanda sun kama barayin da suka shafe shekaru 5 suna satar awaki
Barayin awaki sun ce sun shafe sama da shekara 5 suna satar dabbobi. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Yadda aka kama barayin dabbobin a Neja

An bayyana cewa mazauna yankin da ɓarayin suka addaba da satar ne suka sanya idanu sosai a kansu na tsawon watanni.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Tsallake Rijiya Da Baya Yayin Burtun Da Suka Sha Da 'Yan Daba a Kudo Maso Gabas

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma rahotanni sun nuna cewa, mazauna yankin sun kuma yi ƙoƙarin sanar da jami'an 'yan sanda kan ayyukan ɓarayin da suka addabi unguwannin na su da sata.

Dubun ɓarayin awakin ta cika ne a makon da ya gabata yayin da jami'an 'yan sandan da ke aikin sanya idanu kan sace-sacen suka bi motar ɓarayin har zuwa Shiroro Otal, inda a nan ne suka dafe uku daga cikinsu.

Barayin sun fadi yadda suke shigar da awakin da suka sato

A yayin da suke amsa tambayoyi, kakakin 'yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya ce, ɓarayin sun bayyana cewa sun shafe sama da shekaru biyar suna satar dabbobi a birnin na Minna kuma ba a taɓa kama su ba.

Sun kuma ce suna sayar da awakin da suka sato ne akan naira 10,000 zuwa 15,000 (ya danganta ga girman dabbar), ga mahauta a yankin Maitumbi da kuma Tunga kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici: Dakarun 'Yan Sanda Sun Mamaye Babbar Sakatariyar APC Ta Ƙasa, Bayanai Sun Fito

Wasiu ya ƙara da cewa ɓarayin sun ambaci sunan wasu mutane biyu inda jami'an hukumar suka yi nasarar cafke guda ɗaya daga cikinsu a yayin da ɗayan kuma ya arce.

Soja mace ta bindige oganta a jihar Adamawa

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wata soja da ya sa bindiga ta harbe oganta har lahira a jihar Adamawa.

Mummunan lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga biyo bayan fasa rumbun ajiyar jihar da wasu suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel