Shugaban Sojojin Wagner Ya Mutu a Hatsarin Jirgin Sama a Rasha

Shugaban Sojojin Wagner Ya Mutu a Hatsarin Jirgin Sama a Rasha

  • Shugaban sojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya mutu a wani mummunan hatsarin jirgin sama a Moscow na kasar Rasha
  • Ma'aikatar sufurin jiragen sama ta ƙasar Rasha ta fara bincike kan hatsarin jirgin wada ya auku a yankin Tver ranar Laraba, 23 ga watan Agusta, 2023
  • Jirgin saman na haya ya yi hatsari a Moscow, babban birnin Rasha inda ya yi ajalin mutane 10 ciki har da jagoran sojojin Wagner inji mahukunta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Moscow, Russia - Shugaban rundunar sojoji mai zaman kanta Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya rasa rayuwarsa a wani haɗarin jirgin sama da ya rutsa da shi, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa mutum 10 ne a cikin jirgin sama na haya wanda ya yi haɗari a Arewacin Moscow, babban birnin ƙasar Rasha.

Kara karanta wannan

Wike Ya Bai Wa Yan Kwangila Wata 8 Su Kammala Aikin Layin Dogo Na Zamani a Abuja

Shugaban Wagner, Yevgeny Prigozhin.
Shugaban Sojojin Wagner Ya Mutu a Hatsarin Jirgin Sama a Rasha Hoto: BBC
Asali: Facebook

Ma'aikatar sufurin jiragen sama ta Rasha ta ce fasinjoji bakwai da ma'aikatan jirgin uku ne a cikin jirgin Embraer, wanda ya taso daga Moscow zuwa St Petersburg.

Prigozhin ya wallafa wani faifan bidiyo karo na farko tun bayan abinda ya auku da shi a watan Yuni

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bidiyon ya nuna cewa Prigozhin na cikin nahiyar Afirka kuma ya yi magana kan shirin ƙasar Rasha na tsaftace nahiyar.

An saki bidiyon marigayi shugaban sojojin Wagner a wani dandali a shafin Telegram wanda ke da dangantaka da kamfanin sojojin hayar Wagner.

Shugaban Wagner ya mutu ana tsaka da rikicin Nijar

Wannam bidiyo ya bayyana ne a daidai lokacin da ake fargaba da ɗarɗar a Nahiyar Afirka kan yuwuwar zasu mamaye Jamhuriyar Nijar.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun buƙaci ƙasar Rasha da ta kawo masu ɗauki a yanayin da su ke ciki na yuwuwar yaƙi da ƙungiyar ECOWAS.

Kara karanta wannan

Akpabio Ya Ce Ya Kamata Maza Su Duba Yiwuwar Mika Ragamar Siyasa Ga Mata Su Koma Gefe, Ya Bada Dalili

Ministan Tsaron UK Ya Gana da Hafsoshin Tsaro a Abuja

A wani rahoton na daban Ministan tsaron Burtaniya ya gana da ministocin tsaro da hafsoshin tsaron Najeriya a birnin Abuja ranar Laraba.

James Heappey MP ya jaddada goyon bayan ƙasar Burtaniya ga yunkurin ECOWAS na dawo da mulkin Dimokuraɗiyya a Nijar cikin lumana.

Ya ce Burtaniya ta fahimci kokarin diflomasiyya da Najeriya ke yi na maido da dimokuradiyya a Nijar cikin lumana, ta hanyar kasancewarta mamba a kungiyar ECOWAS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel