Wike Ya Bai Wa Yan Kwangila Wata 8 Su Kammala Aikin Layin Dogo Na Zamani a Abuja

Wike Ya Bai Wa Yan Kwangila Wata 8 Su Kammala Aikin Layin Dogo Na Zamani a Abuja

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ba da wa'adin wata takwas domin a kammala aikin gyaran layin dogo na zamani a Abuja
  • Wike ya ba da wa'adin ne a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta, lokacin da ya ziyarci tashar jirgin kasa ta Abuja da ke Idu da kuma tashar jirgin sama
  • Ziyarar ita ce aikin farko da tsohon gwamnan ya yi a matsayin minista a wajen ofis tun bayan rantsar da shi

FCT, Abuja - A ranar Laraba, 23 ga watan Agusta, ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya bayar da sabon umurni game da aikin layin dogo.

Wike ya yi umurnin kammala aikin layin dogo na Abuja cikin wata takwas
Wike Ya Bai Wa Yan Kwangila Wata 8 Su Kammala Aikin Layin Dogo Na Zamani a Abuja Hoto: Viable Tv
Asali: Facebook

Wike wanda ya nuna bacin rai a kan halin da layin dogon na Abuja ke ciki, ya umurci sakataren dindindin da ya biya kamfanin China da ke aikin cikakken kudi domin a kammala aikin gyaran hanyar jirgin kasan cikin wata takwas, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Makuden Miliyoyi: Farashin Motar Alfarma Ta Wike Mai Lamba 'FCT-01' Ya Bayyana, Yan Najeriya Sunyi Martani

Wike ya ba da wa'adin ne yayin da ya ziyarci tashar jirgin kasan Abuja da ke Idu da tashar jirgin sama a aikinsa na farko da ya yi a wajen ofis, kasa da awanni 48 bayan rantsar da sabbin ministoci 45.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ci gaba da cewa aikin farfado da layin dogon na Abuja ya zama mai muhimmanci daga cikin alkawarin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na rage mawuyacin halin da yan Najeriya ke ciki cikin dan kankanin lokaci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Miliyoyin naira: Farashin motar alfarma ta Wike mai lamba 'FCT-01' ya bayyana

A gefe guda, mun kawo a baya cewa yanayin motar da sabon ministan Abuja da aka rantsar, Nyesom Wike ya hau zuwa wajen aiki a ranarsa ta farko a ofis ya haddasa cece-kuce.

Kara karanta wannan

Albashi Da Allawus Din Ministocin Tinubu Ya Bayyana, Za Su Lakume Biliyan 8.6

A ranar Talata, 22 ga watan Agusta, Wike ya isa babban birnin tarayya a cikin wata tsadaddiyar motar alfarma kirar Lexus LX 600 SUV dauke da lambar ‘FCT – 01’, kuma wannan ya sa mutane da dama tofa albarkacin bakunansu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wani bincike da aka yi a shafin yanar gizon kamfanin Lexus ya sako farashin wannan tsadaddiyar motar SUV din inda ya fara daga $100,115; wanda ya yi daidai da N75,764,028.55.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel