'Yan Najeriya Sun Samu Sauki Yayin da Farashin Gas Ya Ragu a Najeriya Yayin da Fetur Ke Kara Wuta

'Yan Najeriya Sun Samu Sauki Yayin da Farashin Gas Ya Ragu a Najeriya Yayin da Fetur Ke Kara Wuta

 • A karon farko cikin tsawon lokaci, farashin cika tulun iskar gas na girki mai nauyin kilo 5 ko 12.5 ya ragu
 • Sai dai, har yanzu yana da tsada sosai idan aka kwatanta da yadda ‘yan Najeriya suke siyan gas a shekarar 2022
 • Hukumar NBS ta bayyana Bayelsa a matsayin jihar da ta fi kowacce jiha tsada wajen cika tulu mai nauyin kilogiram 5, yayin da Ondo ke da mafi karancin farashi

Hukumar Kididdiga ta Kasa ta bayyana cewa, farashin iskar gas na girki mai mai cika tulu mai nauyin kilo 5 da 12 ya ragu a watan Mayun 2023.

NBS ta bayyana hakan ne a sabon rahotonta na bin diddigin farashi da ta fitar a shafinta na yanar gizo wanda Legit.ng ta samu a karshen makon nan.

Kara karanta wannan

An Samu Matsala: Bene Mai Hawa Uku da Ake Tsaka Ya Aiki Ya Rushe, Bayanai Sun Fito

Bayanai sun nuna cewa matsakaicin farashi a hannun dillalan don cika tulu mai nauyin kilo 5 na gas ya ragu zuwa N4,360.69 a watan Mayun 2023 daga N4,642.27 da aka siya a watan Afrilun 2023.

Yadda farashin gas ya sauka a Najeriya
Frashin gas, kwatancen wata zuwa wata | Hoto: NBS
Asali: Facebook

Duk da haka gas ya karu idan aka kwatanta da bara

A kididdigar shekara zuwa shekara, farashin tulun gas mai nauyin kilogiram 5 ya tashi da 11.20% a watan Mayun 2023 idan aka kwatanta da N3,921.35 da aka sayar a watan Mayun 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, matsakaicin farashin tulu mai nauyin kilogiram 12.5 ya ragu zuwa N9,537.89 a watan Mayu idan aka kwatanta da Afrilun 2023; N10,323.33.

Sai dai kuma farashin ya karu ne da 9.30% daga N8,726.30 da ‘yan Najeriya suka sayi gas a watan Mayun 2022.

Jihohi mafi arha da tsada wajen siyan gas din girki

Hukumar ta NBS ta lissafa jihohin da suka fi kowacce tsada a wajen cika tulun gas mai nauyin kilogiram 5 kamar haka:

Kara karanta wannan

Har An Fara Murna, Sai AA Rano Ya Musanta Karya Farashin Litar Fetur Daga N540

 • Bayelsa - N5,016.67
 • Zamfara - N5,000.00
 • Abuja - N4,900.00

A daya bangaren kuma, jihohin da suka fi arahan gas sun hada da:

 • Ondo - N3,795.83
 • Nasarawa - N3,800.00
 • Edo - N3,837.14

Nazarin farashin a matakin yanki ya kasance kamar haka:

 • Arewa ta Tsakiya - N4,712.85 (mafi tsada)
 • Arewa maso Yamma - N4,550.04
 • Kudu maso Gabas - N4,078.50 (mafi araha)

Gas din girki mai nauyin 12.5kg

Nazarin farashin gas girki mai nauyin kilogiram 12.5 ya kasance kamar haka:

Jihohin da aka fi tsada:

 • Cross River - N11,083.33
 • Jigawa - N10,975.00
 • Akwa Ibom - N10,174.29

Jihohin da aka fi araha:

 • Adamawa - N7,925.00
 • Zamfara - N8,128.57
 • Borno - N8,200.00

Duk wannan tsada da 'yan Najeriya ke fuskanta, akwai kasashen Afrika da yawa da suka fi Najeriya karancin albashi, lamarin da ke kara jefa 'yan kasar cikin wahalhalu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel