Ganin Tulin Jami'an Tsaro Ya Jawo Mutane Sun Shiga Dar-Dar a Arewacin Najeriya

Ganin Tulin Jami'an Tsaro Ya Jawo Mutane Sun Shiga Dar-Dar a Arewacin Najeriya

  • A shiga halin dar-dar bayan tagwayen hare-hare da yan bindiga suka kai jihar Neja wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji da dama
  • Tun bayan faruwar al'amarin an samu karin motocin tsaro da ke sintiri a fadin jihar musamman a babban birnin Minna
  • Sai dai, wani mazaunin garin Minna ya tabbatarwa Legit.ng cewa babu wani abun tashin hankali da suke fuskanta a halin yanzu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Niger - Bayan tagwayen hare-hare da yan bindiga suka kai jihar Neja a daren Lahadi da safiyar Litinin wanda ya yi sanadiyar rasa rayukan sojoji 36, mazauna jihar ta arewa maso tsakiya sun cika da fargaba, jaridar Punch ta rahoto.

An samu karin motocin sojoji da na sauran jami'an tsaro a wurare da dama a babban birnin jihar. An kuma gano manyan motoci cike da sojoji suna tunkarar hanyar Shiroro, karamar hukumar da aka kai hare-haren.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi Ya Tona Masu Karkatar da Shugaba Tinubu da Muguwar Shawara

Jami'an sojoji
An yi amfani da horon don misali ne kawai. Wadanda ke hoton ba su da alaka da batun da ake magana kansa a rahoton. Hoto: Patrick Meinhardt/AFP.
Asali: Getty Images

Haka kuma, an gano tullin motocin fatrol na yan sanda a wuraren jama'a, lamarin da ke nuna cewa hukumomin tsaro suna cikin shirin ko ta kwana ko da wani abun bazata zai taso.

Rundunar yan sandan jihar Neja ta yi martani

Da yake martani kan ci gaban a wata hira da jaridar Punch, kakakin yan sandan jihar, Abiodun Wasiu, ya ce lamari ne da dama akwai shi a kasa tunda yan bindiga suna tayar da zaune tsaye a babban birnin jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa kada a yi tunanin ganin motocin fatrol din yan sanda a wurare masu muhimmanci yana nufin cewa yan sanda suna taka tsan-tsan ne saboda hare-haren da aka kai a karamar hukumar Shiroro.

Abiodun ya ce:

"Babu abun da ke faruwa. Shin abu mara kyau ne don tsaro ya kasance a ko'ina? Kawai dai muna daukar mataki ne don tsaron kowa, babu wani gagarumin abu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Rundunar Sojoji Ta Bayyana Adadin Dakarunta Da Yan Ta’adda Suka Kashe a Neja

"Kuna iya tambayar jama'a, babu abun da ke faruwa. Wannan fatrol din dama chan akwai shi a kasa. Idan kuna bibiyar abubuwan da ke faruwa, bai dade ba da gwamnan ya ba yan sanda da sauran hukumomin tsaro wadannan motocin don tsaurara matakan tsaro a jihar.
"Kawai yana so motocin su kasance a cikin garin ne don a dunga ganinsu. A kalla, kasancewar tsaro a kasa na maganace abubuwa da dama. Wannan na nan tun kafin a kai hare-haren.
“Ku tambayi mutanen gari. An bayar da wadannan motocin a watanni biyu da suka gabata kuma gwamnan ya yi alkawarin wadannan motocin saboda wadannan hukumomin tsaron basu da mota. Don haka, ya kawo su don karfafa fatron din tsaro don haka kada mu fassara abun ya zama saboda abun da ya faru ne.
"Kuna iya zuwa ku yi bincikenku; ta'addanci ya kasance babban kalubale a jihar Neja. Bai da alaka da zuba motocin fatrol a garin. Wannan lamari na fashi da makami a kananan hukumomi biyu ko uku ne."

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Babu wani tashin hankali a Minna, majiya

Legit.ng ta tuntubi wani mazauna garin Minna don jin ta bakinsu game da lamarin.

Mallam Abubakar Bala ya ce:

"Gaskiya ne motocin yan sanda masu suna 'Operation Flush' dama chan suna yawo a garin Minna tun kafin a kai wa sojojin harin. Amma dai duk da aka akwai ranar da muka ga motocin sojoji da dama amma sun mika ne ba wai a cikin garin Minna suka tsaya ba, watakila inda yan fashin suke za su. Amma babu wani abun tashin hankali da ake fuskata a nan cikin gari."

Sojoji 36 aka kashe a jihar Neja, Hedkwatar tsaro

A baya mun ji cewa, a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta, Hedkwatar tsaro, ta bayyana cewa jami'an sojoji 36 aka kashe a jihar Neja.

Darektan watsa labarai na hukumar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayyana adadin mutanen da aka kashe a harin kautan baunar da aka kaiwa sojoji a jihar ta arewa maso gabas a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, Channels TV ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel