Nasir El-Rufai Ya Gargadi Tinubu, Kungiyar ECOWAS Kan Shiga Yaki Da Nijar
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya yi martani kan shirin kungiyar ECOWAS na afkawa Nijar da yaki
- El-Rufai ya ce mutanen Jamhuriyar Nijar daya su ke da 'yan Arewacin Najeriya don haka 'yan uwan juna ne
- Tsohon gwamnan ya bukaci kungiyar ECOWAS da ta kaucewa wannan koma baya na yin yaki a tsakanin 'yan uwan juna
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya gargadi kungiyar ECOWAS kan afkawa Nijar da yaki.
El-Rufai ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Talata 22 ga watan Agusta, Legit.ng ta tattaro.
Wani shawara El-Rufai ya ba Tinubu da ECOWAS?
Ya ce Nijar kasa ce daya kuma 'yar uwar Arewacin Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Nasiru El-Rufai ya kasance na kusa da shugaban kasa, Bola Tinubu inda ya shawarce shi kan matakin soji da kungiyar ECOWAS ke son dauka kan Jamhuriyar Nijar.
Ya kara da cewa Shugaba Tinubu a matsayinsa na jagoran kungiyar ECOWAS ya kamata "ya guji wannan yaki tsakanin 'yan uwan juna".
Meye El-Rufai ya ce kan ECOWAS da Nijar?
El-Rufai ta rubuta a shafinsa kamar haka:
"Yayin da kungiyar ECOWAS ke kokarin yaki da Nijar, na tuna wata waka a 1970 da Dire Straits ya yi, "'Yan uwa cikin makamai" saboda yaki a yanki daya kamar yaki tsakanin 'yan uwa ne.
"Tabbas 'yan Nijar daya su ke da 'yan Arewacin Najeriya, ya kamata mu kauracewa wannan yaki na koma baya tsakanin 'yan uwa."
Idan ba a mantaba sojin kasar Nijar sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ne a karshen watan Yuli kan wasu korafe-korafe a kansa.
Kungiyar ECOWAS a baya ta saka wa kasar Nijar takunkumi bayan sojin kasar sun yi fatali da umarninta.
Shehu Sani Ya Gargadi Tinubu Kan Amfani Da Karfin Sojin ECOWAS
A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya gargadi Shugaba Tinubu kan amfani da karfin soji a kan Nijar.
Sanatan ya bayyana haka ne yayin da kungiyar ECOWAS ke shirin afkawa Nijar da yaki idan sojin kasar ba su mika mulki ga Bazoum ba.
Idan ba a mantaba, sojin Nijar sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a karshen watan Yuli kan korafe-korafe a mulkinsa.
Asali: Legit.ng