Matashi Ya Fashe Da Kuka Yayin da Budurwarsa Ta Ce Masa Bata Da Kowa Bayan Ya Yi Mata Magana Da Wata Lamba

Matashi Ya Fashe Da Kuka Yayin da Budurwarsa Ta Ce Masa Bata Da Kowa Bayan Ya Yi Mata Magana Da Wata Lamba

  • Wani dan Najeriya ya shiga yanayi ayan budurwarsa ta bayyana cewa bata da saurayi, duk da cewar suna soyayya
  • Ya lura cewa bata amsa sakonninsa a WhatsApp sai ya yanke shawarar aika mata sako da wata lamba daban
  • Saurayin da ke cikin takaici ya saki hoton hirarsu da budurwar tasa wanda suka yi da wata lamba daban

Wani matashi dan Najeriya ya koka bayan budurwarsa ta karya masa zuciya ta hanyar bayyana cewa bata da kowani saurayi.

Lamarin ya fara ne bayan ya aika mata sako a WhatsApp a ranar zagowar haihuwarta amma sai ya lura cewa bata amsa masa.

Matashi ya hadu da sharrin soyayya
Matashi Ya Fashe Da Kuka Yayin da Budurwarsa Ta Ce Masa Bata Da Kowa Bayan Ya Yi Mata Magana Da Wata Lamba Hoto: @sammy_sboy
Asali: TikTok

Cike da damuwa, sai ya yi mata magana da wata lamba daban kuma ya sha mamaki lokacin da ta bayyana cewa bata soyayya da kowa.

Kara karanta wannan

Matan zamani: Miji ya sha bulala saboda yiwa matarsa wani babban laifi, jama'a sun girgiza

Matashin da ya karaya ya saki hotunan hirarsu a TikTok yayin da yake nuna rashin jin dadinsa. A cewarsa, ta karya masa zuciya saboda bai da kudi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ta karya mun zuciya da safen nan,” ya koka a soshiyal midiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun tausaya masa

BIGG PAPI ya ce:

"Idan kana neman soyayya ka nemi so yanzu da baka kudi ba za ka samu ba idan ka yi kudi masu son abun hannunka za ka samu dan uwa..."

Lanky ya ce:

"Dan uwa irin abun da na fuskanta kenan..a karshe na rasa ta a wajen gayen da take ce mun abokai ne kawai su...kada ka damu ka gyara zage damtse wajen nemanka. akwai Allah"

Rukky ta ce:

"Kai dan uwa na tayaka jin zafin wannan abu gaskiya na tausaya maka ka yi hakuri dan uwa."

Kara karanta wannan

Arziki nufin Allah ne: Mutumin da ya zauna a Kanada tsawon shekaru 20, ya dawo ba nauyi

KANAYO.O.KANAYO ya ce:

"Ka tabbata idan ka yi asiri sannan ka samu kudi ka yi duk abun da kake so ka hukunta su ka dunga sauya su kamar wando."

A_cumrade ya ce:

"A matsayinka na da namiji kada ka yi tsammanin wani ya tausaya maka ko ya nuna maka damuwa, ka adana damuwarka sannan ka kara zage damtse don samun na kanka, sai ka yi duk abun da kake so."

Budurwa ta dankara hadadden gida tana da shekaru 20

A wani labarin, mun ji cewa wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta cimma muradionta na gina gida da zama mai gidan kanta tun tana da kuruciyarta.

Matashiyar ta dauki hoto a gaban gidan da aka kammala gininsa tare da iyayenta yayin da ta kasance rike da takardun gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel