Matar Aure Ta Fusata, Ta Tsuttsule Mijinta da Bulala Saboda Yawan Jimawa da Yake a Waje da Dare

Matar Aure Ta Fusata, Ta Tsuttsule Mijinta da Bulala Saboda Yawan Jimawa da Yake a Waje da Dare

  • Wata mata ‘yar Najeriya ta harzuka a lokacin da aka gan ta tana yi wa mijinta bulala da tsumagiya mai kyau
  • Yayin da take nuna fushinta cikin raha, ta tsawatar da mijinta kan yadda take fita da daddare ba tare da ya gaya mata ba
  • A bangare guda, jama’a a kafar sada zumunta sun yi martani, inda suka bayyana ra’ayoyinsu game da ma’auratan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata mata ‘yar Najeriya ta yada wani faifan bidiyo inda ta rika yiwa mijinta bulala da tsumagiya saboda ya fiye fita da daddare ba tare da saninta ba.

A cikin faifan bidiyon, mutumin ya sha tuhumar matarsa a lokacin da take yi masa tambayoyi cikin harshen Ibo kan abin da yake aikatawa, kana ta ta umarce shi da ya miko hannunsa ta shauda masa bulali uku.

Kara karanta wannan

Budurwa Yar Shekaru 20 Ta Gina Makeken Gida Harda Ramin Wanka Na Musamman, Ya Hadu Matuka

A bidiyon, an ga yadda yake nuna ya ji zafin karya, inda yake sosa hannun don nuna alamar ya sha bulala mai zafi.

Yadda mata da miji suke wasa
Mata ta zane mijinta da bulala | Hoto: @queendiva984
Asali: TikTok

Bayan tsulaleshi da bulala, sai kuma ta zo tana lallabi tare da jan sa a jiki do nuna kauna da kulawarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a TikTok

Jama’ar kafar sada zumunta sun bayyana kadan daga abin da suka ji game da wannan lamari, ga kadan daga martaninsu:

richloretta:

"Allah ya dawwamar da wannan soyayya da farin ciki a gidanku amin."

user2992822686353:

"Queen diva ke da mijinki kuna ba ni farin ciki sosai."

Shades of jeSsie:

“Cikin girmamawa, malama ba ki da hankali.”

JOMAG:

"Amma me ya kawo bulala a cikin gidanku."

Jenny Quan:

“Ku bar mu mu sarara don Allah muna rokonku.”

mhiz preshy:

"Don Allah wannan aure ne ba wasan yara ba, ka auri aminiyarka za ka gane ya ake ciki."

Kara karanta wannan

Yadda Saurayi Ya Rabu Da Budurwarsa Saboda Ta Yi Yunkurin Shiga Kundin Bajinta Na Guinness, Ya Ce Ta Kunyata Shi

mhizamy965:

"Wanda yace soyayya ba abu ne mai kyau ba
"Zo ka tambayi diva."

Diya ta rama wa uba

A wani labarin, wata uwa, #mafaldagomes004, ta wallafa wani bidiyo mai ban dariya a dandalin TikTok don nuna yadda 'diyarta ke kula da mahaifinta da kuma irin shakuwar dake tsakaninsu.

A wani gajeren bidiyo, mahaifiyar ta nuna kamar tana fada da mijinta wanda yake dauke da 'yar yarinyar. A lokacin da mahaifiyar ta kama hannun mutumin kamar tana dukansa, yarinyar ta shigar mishi fadan.

A matsayin hanyar dakatar da mahaifiyar, 'yar yarinyar ta ciji mahaifiyarta a hannu. Mutane da dama sun yi mamakin matakin da yarinyar ta dauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel