Hukumar NBTE Ta Kaddamar Da Karatun Mayar Da Kwalin HND Zuwa Na Digiri Cikin Shekara 1

Hukumar NBTE Ta Kaddamar Da Karatun Mayar Da Kwalin HND Zuwa Na Digiri Cikin Shekara 1

  • Hukumar ilmin ayyukan hannu (NBTE) ta ƙaddamar da wani sabon shiri domin cike giɓin da ke tsakanin masu kwalin HND da na digiri
  • Hukumar NBTE ta sanar da cewa wannan sabon tsarin zai ba masu kwalin HND damar mallakar kwalin digiri
  • Masu kwalin HND dai suna fuskantar wariya wajen ɗaukar aiki a Najeriya inda ake fifita masu kwalin digiri a kansu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Hukumar ilmin ayyukan hannu (NBTE) a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, ta ƙaddamar da wani shirin karatu a yanar gizo ga masu kwalin HND ta yadda za su mayar da kwalayensu zuwa na digiri (BSc).

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, Mrs Fatima Abubakar, ta fitar a birnin tarayya Abuja.

NBTE ta kaddamar da shirin karatun mayar da HND zuwa digiri
A karkashin sabon karatun masu kwalin HND za su samu digiri cikin shekara daya Hoto: Covenant University
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa hukumar ta yi bayanin cewa wahalar da masu kwalin HND su ke sha na wajen ƙin ba su matsayin da ya dace, na daga cikin manyan dalilin da ya sanya ta fito da wannan sabon tsarin.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: An Fadawa Tinubu Abu Daya Tak Da Zai Yi Don Shawo Kan Matsalar Tsaro A Jihar Arewa, Ta Nemi Bukata

Mayar da kwalin HND zuwa na Digiri a Najeriya

Tun da farko hukumar a ranar Lahadi, 13 ga watan Agusta, ta fitar da sabbin bayanai kan sabon shirin a shafinta na Facebook.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Ƙoƙarin da aka yi a baya na hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa ta amince da karatun digirin digirgir na shekara biyu ga masu kwalin HND a wasu kwalejojin fasaha bai haifar da ɗa mai ido ba."
"Masu kwalin HND sai sun yi karatun shekara ɗaya na (PGD) kafin su samu gurbin yin karatun digirin digirgir a jami'a. Abin takaici wannan hanyar ta PGD cike take da matsala inda ko waɗanda suka yi karatun digirin digir daga baya ana buƙatar sai sun kawo kwalin digirinsu na farko."
"Domin magance waɗannan matsalolin, hukumar NBTE ta ƙaddamar da sabon fotal domin shirin wanda za a iya shiga ta nan https://topup.nbte.gov.ng.”

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

Sanata Zai Biyawa Dalibai Kudin Jami'a

A wani labarin kuma, Sanatan Kano ta Tsakiya, ya shirya ware N20m domin biyawa ɗalibai kuɗin karatu a jami'a.

Sanata Rufai Hanga na jam'iyyar NNPP zai biyawa ɗaliban kuɗin karatun ne biyo bayan ƙarin kuɗin makaranta da jami'ar Bayero da ke Kano ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel