ECOWAS Ta Ce Za Ta Ɗora Alhakin Duk Abinda Dakarun Wagner Suka Yi Kan Kasar Rasha

ECOWAS Ta Ce Za Ta Ɗora Alhakin Duk Abinda Dakarun Wagner Suka Yi Kan Kasar Rasha

  • ECOWAS ta aika da saƙon gargaɗi ga dakarun sojojin haya na Wagner dangane da rikicin Nijar
  • ECOWAS ta za ta ɗora alhakin duk wani abu na take haƙƙin ɗan adam da Wagner ta yi a kan ƙasar Rasha
  • Ta ƙara da cewa ba ta son ganin wasu jami'an tsaro masu zaman kansu na shiga cikin lamuran yankin Afrika ta Yamma

Kungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), ta ce za ta ɗora alhakin duk wasu ayyuka na take haƙƙin ɗan adam da dakarun sojin haya na Wagner suka yi dangane da rikicin jamhuriyar Nijar.

Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Ambasada Abdel-Fatau Musah ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels ranar Juma'a.

ECOWAS ta gargaɗi ƙasar Rasha kan juyin mulkin Nijar
ECOWAS ta gargaɗi ƙasar Rasha kan katsalandan a rikicin Nijar. Hoto: Presidency/@KremlinRussia_E/@General_Tchiani
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Yi, Sun Bayyana Ranar Dawowa Bakin Aiki

“Zamu ɗora alhakin duk abinda Wagner ta yi a kan Rasha”

Musah ya ce yanzu haka dakarun na Wagner na can a ƙasar Mali, saboda akwai wani ƙulli da suka yi tsakanin gwamnatin Mali da ƙasar Rasha.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa muddun dakarun na Wagner, waɗanda mallakin Rasha ne suka yi wani abu na take haƙƙin bil'adama, to babu wanda ECOWAS za ta ɗorawa alhakin sai ƙasar Rasha da kuma ƙasar da ta ɗauko hayarsu.

Ya ce yanzu ƙasashen Afrika ba sa buƙatar irin waɗannan dakarun na haya masu zaman kansu a nahiyar, kuma duk wani abu da suka yi, alhakin zai rataya a wuyan ƙasashensu na asali.

“Ba ma son katsalandan ɗin Wagner a ƙasashen Afrika”

Musah ya ƙara da cewa ba za su bari Afrika ta Yamma ta zama filin da wasu ƙasashen duniya za su gwada ƙarfin makamansu ba.

Kara karanta wannan

Shugaban Kwaddibuwa Ya Ayyana Sojojin Nijar a Matsayin 'Yan Ta'adda, Ya Fadi Abinda Ya Kamata a Yi Mu Su

A kalamansa:

“Ba ma san wasu dakarun haya na kamfanoni masu zaman kansu su riƙa yin katsalandan cikin rikice-rikecen da ke faruwa a nahiyar Afrika.”
“Mun riga da mun san illar da shigowarsu cikin lamuran za ta iya haifarwa.”

Amurka ta gargaɗi Nijar kan taɓa lafiyar Bazoum

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da ƙasar Amurka ta yi wa sojojin Nijar na cewa kar su kuskura su taɓa lafiyar Bazoum.

Amurka ta kuma gargaɗi sojojin na Nijar da suka yi juyin mulki da kar su taɓa lafiyar iyalan Bazoum ko wani daga cikin ministocinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel