An Doke Dangote A Matsayin Wanda Ya Fi Arziki A Afirka A Rahoton Forbes, Dan Afirka Ta Kudu Ya Karbi Matsayin
- Alhaji Aliko Dangote ya rasa matsayinsa na wanda yafi kowa kudi a Nahiyar Afirka gaba daya, a rahoton Forbes da ta cire
- Dangote ya rasa matakin ne ga wani mai arziki na kasar Afrika ta Kudu, Johann Rupert wanda yanzu shi ne yafi kowa kudi a Nahiyar Afirka
- Dangote ya rike wannan matsayi na wanda yafi kowa arziki a Nahiyar Afirka fiye da shekaru 10 kafin wannan lokaci da Rupert ya doke shi
Shahararren mai arziki na Najeriya, Alhaji Aliko Dangote ya rasa matsayinsa na wanda yafi kowa kudi a Nahiyar Afirka.
Forbes ta tattaro cewa ya samu raguwar $3.4bn a rana daya saboda faduwar darajar Naira, wanda hakan ya jawo wa masu kudi da dama asara a kasar.
![Dangote ya zama na biyu a masu arzikin Nahiyar Afirka Dangote ya zama na biyu a masu arzikin Nahiyar Afirka](https://cdn.legit.ng/images/1120/24f89aa2bd872aa0.jpeg?v=1)
Asali: Getty Images
Yanzu Aliko Dangote ya sauko mataki na biyu kamar yadda jerin Forbes ya nuna, yayin da attajirin kasar Afirka ta Kudu Johann Rupert ya dare matakin farko.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/25de7ea03db5b7f9.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Zance ya fito: Bayan Ganawar Tinubu Da Dangote Da Matawalle, Batutuwa Sun Fito Waje
Forbes ta kimanta yawan kudaden Dangote da Rupert
Forbes ta kimanta arzikin Rupert da cewa ya kai $12bn, yayin da 2014 Forbes ta kimanta kudaden Aliko Dangote da cewa ya fi $20bn.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dangote ya kai shekaru 12 yana rike da kambun wanda yafi kowa arziki a Nahiyar Afirka, cewar Legit.ng.
Rahotanni sun tabbatar da cewa dukiyar Dangote ta ragu daga $25bn a 2014 zuwa $14.2bn saboda matsalolin karyewar darajar Naira a kasuwanni.
Bloomberg ta ce har yanzu Dangote ne mafi arziki a Nahiyar Afirka
Har ila yau, Dangote ne mafi arziki a Nahiyar Afirka a jerin sunayen da Bloomberg ta fitar, amma ya sauko daga cikin mutane 100 mafi arziki a duniya.
Bloomberg ta kimanta arzikin Dangote akan $16.8 a matakin farko yayin da Rupert ta kimanta arzikinsa akan $13.3 a mataki na biyu.
Baya ga Dangote, shahararrun masu arziki a Najeriya su ma sun ji wuya dalilin faduwar darajar Naira a kasuwanni.
Wanda yafi kowa kudi a Najeriya bayan Dangote shi ne Abdul Samad Rabiu sai kuma mai biye masa Mike Adenuga.
Dangote, Bill Gates Za Su Gana Da Tinubu A Ranar Litinin
A wani labarin, shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana ziyarar da za su kawo fadar shugaban kasa, Bola Tinubu.
Dangote ya ce za su kawo ziyarar ne a ranar Litinin 19 ga watan Yuni mai zuwa wurin shugaban kasa.
Ya bayyana haka ne bayan ya yi wata ganawar sirri da Shugaba Bola Tinubu a ranar Juma'a 16 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng