Tawagar Majalisar Koli Ta Shari’a Ta Gana Da Shugaban Kasa Tinubu, Cikakken Bayani Ya Bayyana

Tawagar Majalisar Koli Ta Shari’a Ta Gana Da Shugaban Kasa Tinubu, Cikakken Bayani Ya Bayyana

  • Mambobin majalisar koli ta Shari'a a Najeriya sun gana da Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta
  • Shugaban kasar ya tarbi shugabannin Musuluncin a zauren fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Koda dai ba a san cikakken dalilin ganawar tasu ba amma wannan shine karo na farko da malaman musuluncin ke ganawa da shugaban kasar tun bayan da ya hau mulki

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da mambobin majalisar koli ta shari'a a Najeriya a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta.

Tawagar majalisar koli ta shari'a sun ziyarci Shugaban kasa Tinubu
Yanzu Yanzu: Tawagar Majalisar Koli Ta Shari’a Sun Gana Da Shugaban Kasa Tinubu, Cikakken Bayani Ya Bayyana Hoto: NTA News @NTANewsNow
Asali: Twitter

Dalilin da yasa majalisar koli ta Shari'a ta ziyarci Tinubu

Kamar yadda NTA News ta rahoto, ba a bayyana cikakken bayanin ganawarsu va amma Legit.ng ta fahimci cewa wannan shine karo na farko da malaman Musuluncin ke ganawa da Tinubu tun bayan da ya hau karagar mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Cikakkun Sunayen Ministocin Da Majalisar Dattawa Ta Tabbatar, Jihohi Da Yankunansu

Bayanai game da majalisar koli ta shari'a

Majalisar koli ta Shari'a wata kungiya ce ta malamai da shugabannin Musulunci a Najeriya. An kafa ta ne a 1990 domin bunkasa koyarwar addinin Islama da kuma kare hakkin Musulmai a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tantance ministoci: Kada ka rantsar da El-Rufai, Malaman Musulunci sun gargadi Tinubu

Legit.ng ta rahoto a baya cewa gamayyar kungiyar makaranta da mahaddatan Al-Qur'ani sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sannan sun gabatar da wani babban bukata a gabansa.

Malaman Musuluncin sun bukaci shugaban kasa Tinubu da kada ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai a matsayin minista a majalisarsa saboda adalci, gaskiya, zaman lafiya da dorewar kasar nan.

Da yake magana da manema labarai a Bauchi a madadin malaman, daraktan kula da ilimi na gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Sidi Aliyu Sise, ya shawarci Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan sannan kada ya rantsar da azalluman yan siyasa da ke da kuntun kashi a tsuliyarsu.

Ya ce zabar El-Rufai da tantance shi da majalisar dokokin tarayya ta yi rashin adalci ne ga masu karatu da masu haddar Al-Qur'ani saboda tauye su da ya yi a lokacin da yake matsayin gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng