Daga Sukari Zuwa Siminti: Harkallar Kasuwnaci 9 Mallakin Attajirin Nan Banako, Abdulsamad Rabiu

Daga Sukari Zuwa Siminti: Harkallar Kasuwnaci 9 Mallakin Attajirin Nan Banako, Abdulsamad Rabiu

Najeriya gida ne ga attajiran ‘yan kasuwan da suka ciri tuta a duniya, daga cikinsu akwai mai kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu.

Kamfanin na BUA, wanda ya yi fice wajen harkallolin kasuwanci daban-daban a Najeriya, ya samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya da dama har ma da ‘yan kasashen ketarae.

A baya-bayan nan, rahotonmu ya bayyana yadda Abdulsamad Rabiu yake tashe da kuma yadda kamfaninsa ke kara samun karbuwa a gida da ma kasashen ketare na makwabta.

Amma a wannan karon, duba za mu yi ga yadda kamfanin BUA Group ya karkasu zuwa bangarori daban-daban na harkallolin kasuwanci.

Kayayyakin kasuwancin BUA
Abdulsamad Rabiu, mai kamfanin BUA | Hoto: Abdulsamad Rabiu
Asali: Facebook

Masana’antar sukarin BUA

Kamfanin BUA na daya daga cikin masu samar da kayan sukari a Najeriya, wanda a shekarar 2018 ne BUA ya saye kamfanin Lafiagi Sugar Company Ltd (LASUCO) da ke jihar Kwara ya hade da nasa.

Kara karanta wannan

To fah: Saura kwana 8 Buhari ya sauka, ya kori babban daraktan FAAN, ya nada sabo

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bugu da kari, kamfanin ya kafa kamfanin Bassa Sugar Company a jihar Kogi. Don tabbatar da tafiyar da harkallar kayan sukari ba kakkautawa, BUA ya samar da gonaki masu girman akalla hekta 70,000 don noman rake.

Idan tsare-tsaren kasuwancin BUA na sukari ya kankama, zai kawo habakar tattalin arziki da habaka fannin kasuwancin kamfanin kansa.

Masarrafar sukarin BUA

BUA Group na da manyan masarrafan sukari guda biyu; daya a jihar Legas, daya kuma a Fatakwal, wadanda ke samar da sukarin da ya kai manyan tan 1,500,000.

Wadannan masarrafan sukari na amfani da fasahar zamani wajen samar da sukarin amfanin yau da kullum da kuma na kamfanoni da ake sake sarrafawa.

BUA ne ke da masarrafar sukari ta farko a Najeriya wacce ke wajen jihar Legas kuma mai samar da adadin da ake bukata.

Kara karanta wannan

A sharar titi: Yadda wata mata ke hada sama da N860k a sana'ar shara

Masana’antar fulawa

Garin fulawa na daya daga cikin abubuwan da ke da tasiri matuka a fannin abinci a Najeriya. A halin da ake ciki, ana amfani da fulawa a burodi, garin tuwon semolina, taliya da sauran abubuwa da kaso 60%, 20%, 10% da 10% bi da bi.

Alkama, ita ce babban abin da ya fi yawa wajen samar da fular burodi, cincin, taliya, garin tuwon semolina da dai sauran abinci ke da bukatar kusan kaso 99% na garin.

Akalla, ana bukatar shigo da manyan tan miliyan 5.67 na wannan gari na fulawar abinci zuwa cikin Najeriya.

Don cike gurbin bukatar fulawa, tsagin kamfanin BUA, IRS ya samar da wurin sarrafa fulawa a birnin Fatakwal a jihar Ribas.

Man gyaran BUA

Haka nan, wannan kamfani an IRS ne ke samar da taliyar IRS ta BUA da ta yi fice a cikin Najeriya da kasashen waje.

A shekarar 2001, kamfanin BUA ya saye kamfanin Nigeria Oil Mills Ltd da aka bude a 1951.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hawaye, Bakin Ciki Yayin Da Wanda Ya Kafa FCMB Ya Rasu, Bayanai Sun Fito

Hadewar kamfanonin biyu; Nigeria Oil Mills da ke Kano da kuma BUA Oil Mills da ke Legas, suna samar da mai daga gyada, ‘ya’yan auduga da ma dai sauraran kayayyaki, ciki har da abincin dabbobi da sabulu.

Sashen shinkafa na BUA

BUA Group ya kafa masana’antar shinkafa da ke noma akalla hekta 10,000 na shinkafar da ake ci a kasar nan.

Kamfanin da ke Kano kuma mafi tsada a jihar, yana samar da hanyoyin cike gibin abinci, musamman shinkafa a Najeriya.

BUA Group na kuma da tsarin damawa da manoma, inda ya hada kai da manoma sama da 100,000 a jihohin Kano da Jigawa don samar da shinkafa.

A halin da ake ciki, yana iya samar da tan na shinkafa 200,000 a shekara, kuma yanzu haka ana aikin gyara yadda zai iya samar da akalla manyan tan miliyan 1 akalla a shekara.

Simintin BUA

Kamfanin simintin BUA na daya daga cikin kamfanonin da ke samar da simintin gini a Najeriya, a jihohin Kudu da Arewa.

Kara karanta wannan

Yadda Muka Rasa ’Yan Uwanmu a Harin ’Yan Bindiga, Mutane Sun Koka a Jihar Plateau

Kamfanin na samar da siminti nau’ika daban-daban, daidai da bukatar gida Najeriya da kuma ingancin da ake bukata a duniya.

BUA Ports & Terminals

A karkashin reshen BUA Ports & Terminals, BUA Group ya samu hakkin mallakar Terminal 'B' na Hukumar Tashoshin Ruwan Najeriya, dake jihar Ribas a Najeriya.

A wannan sashe, BUA na harkallar shiga da ficen kayayyaki a Najeriya kamar yadda wasu kasuwanni ke dashi.

Kamfanin karfe na BUA

Kamfanin BUA Group, ta reshensa na BUA Iron & Steel Ltd na magance kalubalen karfe a Najeriya tare da kafa kamfanin sarrafa karafa mai karfin samar da karfe tan miliyan 1 a shekara.

Harkar gine-gine na BUA

Duba da yadda ake ci gaba da bukatuwa ga fannin samar da gidaje, kamfanin BUA ya tsunduma harkar dillacin gine-gine na gidaje, kasuwanci da sauran harkokin gina birane.

A bangare guda, Dangote, abokin goyayyar Abdulsamad na kasuwanci kuma 'yan jiha daya yana da karkokin kasuwanci makamantan wadannan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel