Hukumar DSS Ta Ce Ta Bi Umarnin Kotu Kan Ci Gaba Da Tsare Emefiele, Bawa Da Nnamdi Kamu

Hukumar DSS Ta Ce Ta Bi Umarnin Kotu Kan Ci Gaba Da Tsare Emefiele, Bawa Da Nnamdi Kamu

  • Hukumar DSS, ta musanta zarge-zargen da ake ma ta na cewa ba ta bin umarnin kotu
  • Hukumar ta ce ta bi duk umarnin da ya kamata a kan Emefiele, Bawa da kuma Nnamdi Kanu
  • Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya fitar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Hukumar jami'an tsaro na farin kaya (DSS), ta musanta zarge-zargen da ake yi ma ta na cewa tana ƙin bin umarnin kotu a lokuta da dama.

Hukumar ta ce ta bi umarnin kotu a kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrashid Bawa, da kuma shugaban 'yan asalin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Peter N. Afunanya ne ya bayyana hakan cikin wata zungureriyar wasiƙa ranar Litinin, kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Kara karanta wannan

Ku Yi Hakuri: Shugabannin 'Yan Bindiga a Arewa Sun Nemi Afuwa, Za Su Ajiye Makamai

Hukumar DSS ta yi ƙarin haske kan dalilin ci gaba da tsare Bawa, Emefiele da Kanu
Hukumar DSS ta ce ba ta taka wata doka ba kan ci gaba da tsare Emefiele, Bawa da Kamu. Hoto: Intel Region
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

DSS ta bi umarnin kotu kan Emefiele, Bawa da Kanu

Ya bayyana cewa hukumar DSS ta bi umarnin kotu kuma ta tafiyar da lamurran yadda suka dace a kan mutanen da suke tsare da su.

Ya ce hukumar ta tafiyar da komai daidai da yadda dokar Najeriya ta tanada, inda ya shawarci masu suka da su zurfafa bincike dangane da hakan.

Ya ƙara da cewa kotu ta sha dakatar da hukumar daga kama gwamnan babban bankin duk kuwa da irin girman laifukan da hukumar ke tuhumarsa da su kamar yadda The Cable ta wallafa.

Daga cikin laifukan da hukumar ta DSS ke tuhumar Emefiele akwai ɗaukar nauyin ta'addancin.

DSS ta musanta batun sakin Nnamdi Kanu

A baya Legit.ng ta kawo muku cewa hukumar DSS ta musanta raɗe-raɗin da ake na cewar ta saki shugaban ƙungiyar 'yan asalin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Soja mace ta fusata, ta harbe na gaba da ita a wurin aiki a jihar Arewa

Hukumar ta ce ta bi umarnin wata kotu ne kawai na barin likitoci su duba lafiyarsa kamar yadda lauyansa ya buƙata.

Shugaban 'yan awaren ya kasance a tsare tun lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Falana ya bukaci DSS ta yi gaggawar kamalla bincike kan Bawa da Emefiele

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan buƙatar da babban lauya mai fafutukar kare haƙƙin bil'ama Femi Falana ya miƙa ga hukumar DSS, na ta yi gaggawar kammala bincike kan Bawa da Emefiele.

Falana ya ce ci gaba da ajiye su da hukumar ta DSS ke yi a hannunta, ya saɓawa dokokin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel