Sanatocin Najeriya Sun Ki Amincewa da Bukatar Tinubu Na a Tura Sojojin Najeriya Su Yaki Na Nijar

Sanatocin Najeriya Sun Ki Amincewa da Bukatar Tinubu Na a Tura Sojojin Najeriya Su Yaki Na Nijar

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Sanatocin Najeriya basu amince da batun amfani da sojojin Najeriya a yaki na Nijar ba
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ECOWAS ta ce za ta dauki mataki kan wadanda suka yi juyin mulki a Nijar
  • A baya kun ji cewa, an yi juyin mulki a Nijar, lamari da ke kara yiwa dimokradiyya barazana a nahiyar Afrika

FCT, Abuja - Sanatocin Najeriya sun yi watsi da bukatar da Shugaba Bola Tinubu na neman izinin tura sojojin Najeriya zuwa jamhuriyar Nijar a matsayin wani bangare na muradin ECOWAS na maido da zababben Shugaban kasar Mohamed Bazoum.

An hambarar da Shugaba Bazoum ne a ranar 26 ga watan Yuli a wani juyin mulki karkashin jagorancin masu gadin fadar shugaban kasar, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Hambararren Shugaban Nijar Bazoum Ya Aike da Sabon Saƙo Ga Amurka da Wasu Ƙasashe

Shugabannin ECOWAS a wani taro da suka yi a Abuja kwanaki hudu bayan haka sun ba wadanda suka yi juyin mulkin wa’adin kwanaki bakwai su maido da Bazoum kan kujerarsa.

Sanatoci sun ki muradin Tinubu
Yadda aka yi zaman ECOWAS da Shugaba Tinubu | Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

An kakaba wa Nijar takunkumi

ECOWAS ta kuma kakaba takunkumi kan sabon mulkin na Nijar, inda ta umarci katse wutar lantarkin da Nijar ke mora daga Najeriya da kuma rufe iyakokinta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, ECOWAS karkashin Shugaba Tinubu ta yi barazanar tura sojojinta zuwa Nijar domin kwace mulkin, wanda daga ciki har da sojojin Najeriya.

Sai dai, a zaman da suka yi a ranar Asabar 5 ga watan Agusta, Sanatocin sun yi watsi da bukatar shugaban kasar na tura sojojin Najeriya Nijar.

A cewar wani sanatan da ya halarci taron, Sanatoci sun amince da zartas da kudurin yin Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar din.

Kara karanta wannan

A Duba Dai: Sanatocin Arewa Ba Su Yarda Tinubu Ya Shiga Yaki Da Kasar Nijar Ba

Sanatoci sun yabi Tinubu bisa daukar mataki kan sojojin Nijar

Hakazalika, sun yabawa Shugabannin kungiyar ECOWAS kan kokarin da suke yi na maido da tsarin mulkin dimokradiyya a Nijar, amma sun yi watsi da zabin amfani da akrfin sojoji.

Premium Times ta ruwaito cewa, 90% na Sanatocin kasar gaba daya basu amince da yin amfani da karfin soja kan Nijar ba.

Saboda haka, majalisar ta ce bata amince da batun tura soja, amma ta amince da kokarin Tinubu na kakaba takunkumi.

ECOWAS ta tura 'yan sasanci zuwa Nijar

A wani labarin, kungiyar raya kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), ta tura tawagar sasanci zuwa jamhuriyar Nijar don tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin tsaron kasashen na ECOWAS ke gudanar da taro kan yadda za a bullowa lamarin Nijar din a Abuja.

Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da harkokin tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah ne ya shaidawa manema labarai hakan a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Jamhuriyar Nijar Ta Ɗauka Mataki Mai Tsauri Kan Najeriya da Wasu Ƙasashe Bayan Sulhu Ya Rushe

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel