Kwankwaso da Jerin Mutum 10 da Za a Saurari Sunayensu a Sahun Karshen Ministoci

Kwankwaso da Jerin Mutum 10 da Za a Saurari Sunayensu a Sahun Karshen Ministoci

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu bai gama zakulo wadanda za su zama Ministoci a gwamnatinsa ba
  • Ana sa ran nan gaba Shugaban kasar ya aikawa Majalisar dattawa karin sunayen fiye da mutane 10
  • A hasashenmu, Rabiu Kwankwaso, James Faleke da Aishatu Dahiru Ahmed za su iya tashi da kujera

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

1. Aishatu Dahiru Ahmed

Babu mamaki Sanata Aishatu Dahiru Ahmed ta samu kujerar Minista idan ta tabbata ba za tayi nasara a kotun zaben Adamawa ba, hakan zai ba mata karin mukamai a gwamnati.

2. Timi Alaibe

Idan kura ta lafa a Bayelsa, Bola Ahmed Tinubu zai iya dauko Timi Alaibe musamman ganin ya shugabanci hukumar NDDC kuma ya yi aiki da manyan kamfanoni a Najeriya.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu bai gama nada Ministoci ba Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Dalilan da Suka Jawo Babu Minista ko 1 Daga Kano, Filato da Legas a Sahun Farko

3. Mukhail Adetokunbo Abiru

Mukhail Adetokunbo Abiru kwararren ma’aikacin banki ne da zai iya samu kujera a gwamnati mai-ci, yanzu haka shi ne Sanata mai wakiltar Gabashin Legas a majalisar dattawa.

4. Abubakar Inuwa Kari

Abubakar Inuwa Kari ne wanda ya canji Muhammed Kabir Usman Kukan a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Gombe, watakila ya zama Ministan tarayya.

5. Akinwumi Ambode

Idan Legas za ta samu kujerun Ministoci biyu, babu mamaki a dauko tsohon Gwamna Akinwumi Ambode, akwai yiwuwar dawo da Babatunde Fashola wanda ya yi Minista a baya.

6. Rabiu Musa Kwankwaso

Kofa a bude ta ke ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ko kuwa wani daga cikin ‘ya ‘yan NNPP su samu mukami, hakan ya danganta da siyasa da shari'ar zaben jihar Kano.

7. Abiodun James Fakele

Shugaban kwamitin tattalin arziki a majalisa, Abiodun James Fakele zai iya shiga jerin Ministoci, na hannun daman shugaban kasa ne kuma shi ne sakataren yakin zabensa.

Kara karanta wannan

Ganduje da Tsofaffin Gwamnoni 7 da Tinubu Ya Watsar Wajen Rabon Mukaman Minista

8. Gboyega Oyetola

Tsohon Gwamnan na Osun yana da kusanci sosai da shugaban kasa, Legit.ng Hausa ta na ganin za a nada Gboyega Oyetola Minista domin rage zafin zaben da ya rasa ga PDP.

9. Simon Lalong

Har yanzu shugaban kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu bai samu mukami ba, kuma Simon Bako Lalong ya rasa takarar Sanata Filato ta Kudu ga AVM Napoleon Bali.

10. Bachir Sheriff Machina

A hasashen Legit.ng Hausa, Bachir Sheriff Machina zai iya zama Minista ganin yadda aka yi masa kwalelen kujerar Sanatan Yobe ta Arewa, ya dade tare da Tinubu a siyasa.

11. Kabiru Marafa

PDP ta doke Gwamnan Zamfara da Sanata Kabiru Marafa a zaben 2023, watakila tsohon ‘dan majalisar ya zama Minista musamman ganin babu zargin EFCC tattare a shi.

Jihohi 11 ba su da Minista

Kun ji labari Bola Tinubu ya rasa yadda zai yi rabon kujerar Ministan Kano tsakanin Kwankwasawa da ‘Yan Gandujiyya, musamman da ya ba Katsina kujeru biyu.

A mahaifar shugaban Najeriya, har yanzu ba a game yanke shawara ba. Akwai inda shugaban kasa ya zabi Minista, amma ‘yan jihar su ka nuna ba haka su ke so ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel