Hanyoyi Guda 4 da Mutum Zai Bi Wajen Kare Kai Daga Farmakin ’Yan Ta’adda a Najeriya
Cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ya kai ga ‘yan Najeriya sun fada cikin hadari da tashin hankalin kuncin rayuwa.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Hakan ka iya jawo karuwar ta’addanci, yankan aljihu, sace-sace da ma duk wasu ayyukan ta’addanci don samun yadda za a kai abinci bakin salati.
Hakazalika, taku da kafa zai karu kasancewar ba kowa ne zai iya biyan daruruwan kudade ba wajen zirga-zirga.
Wani masanin tsaro, Auwal Bala Durumin Iya ya ba da shawarwari kan yadda mutum zai kare kansa daga farmaki idan ta kama.
Ga abubuwan da masanin ya bayyana kan yadda za a kare kai daga tasirin bakar wahalar da ake ciki a yanzu, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tsaron dan adam
Bala ya ce tsaron dan Adam na nufin sanin barazanar tsaro da ke zagaye da muhallin da mutum ke rayuwa.
"Akwai bukatar sanin iskar da kuke shaka, ruwan da kuke sha da sauran abubuwa a waje wadanda zasu iya zama barazana ga rayuwar ku. Babu wanda zai iya ba ku irin wannan tsaro, sai ku kanku.”
Lokacin fita, musamman da daddare kuma a wuraren da suke shuru, yana da kyau mutum ya kasance tare da wani. Akwai wahala ‘yan ta’adda su iya farmakar mutane da yawa.
Idan kai kadai kake tafiya, ka tabbatar ka san motsin da ke kusa da nesa da kai ta hanyar bin hanyoyin da akwai jama’a da kuma wuraren da ke da haske.
Tsaron al'umma
A cewar masanin tsaron, tsaron al'umma na nufin haduwar gungun mutane don kare kansu daga barazanar da ke kusa da su.
Wannan ya hada da duk wata tattaunawa tsakanin mazauna unguwa ko yanki don tabbatar da cewa al’ummar da mazauna cikinta sun kubuta daga barazanar tsoro.
Kare kai
Kare kai wani mataki ne da ya kunshi koyon wasu dabaru na kare kai daga cutarwa ta jiki.
Misali, mutum ya koyi yadda ake tare naushi, mari ko shura; ko yadda ake kubuta daga hatsari idan ta taso.
Kula da hali
Kyawawan halaye da dabi’u suna hana mutum shiga cikin cakwakiya. Wannan na nufin idan mutum na da kyawawan halaye, ba zai yiwu ka saba ka'idoji da kimar al'ummar da kake rayuwa da ita ba.
A cewar Durumin-Iya:
"Ta hanyar bin ka'idoji da kare kimar al'ummar da rayuwa da ita, kana kare kan ka ne daga hare-hare a kaikaice.”
Tinubu zai sama wa 'yan Najeriya aiki a Google, ya fadi ta yaya
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana shirin gwamnatin Najeriya na aiki da katafaren fasahar Google don samar da ayyukan yi na zamani miliyan daya a kasar.
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai baiwa shugaba Tinubu shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake, shugaban ya ba da wannan tabbacin ne a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a 28 ga watan Yuli, 2023.
Legit.ng Hausa ta gano cewa, Tinubu ya yi wannan batu ne a lokacin da mataimakin shugaban kamfanin Google na duniya Richard Gingras ya ziyarci ofishinsa.
Asali: Legit.ng