Sojoji Sun Halaka Yan Ta’adda 59, Sun Ceto Mutane 88 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Halaka Yan Ta’adda 59, Sun Ceto Mutane 88 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka 'yan ta'adda 59 a yayin samame da jami'an suka kai a fadin kasar
  • Manjo Janar Edward Buba, Daraktan yada labarai na rundunar tsaron, shi ya bayyana haka ga 'yan jaridu a Abuja
  • Ya ce rundunar ta kama masu laifuka daban-daban 88 da masu garkuwa 10 sai kuma 'yan bindiga 20 da kuma masu fasa bututun mai 19

FCT Abuja - Rundunar sojin Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda fiye da 50 a samame daban-daban da rundunar ta yi a wurare da dama na fadin kasar.

Rundunar ta kuma kubutar da mutane fiye da 80 daga hannun masu garkuwa kamar yadda hedikwatar tsaro ta tabbatar.

Sojoji sun sheke 'yan ta'adda da dama yayin da suka kubutar mutane 88 da aka yi garkuwa da su
Rundunar Sojojin Najeriya Sun Halaka Yan Ta’adda Da Dama Tare Da Kubutar Da Wasu, Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba shi ya bayyana haka a yau Juma'a 28 ga watan Yuli a Abuja, cewar PM News.

Kara karanta wannan

Hankula Sun Tashi Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Bindige Wasu Dalibai A Shagon Aski, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

Rundunar ta kama 'yan ta'adda 59 da kubutar da wasu 88

Ya ce rundunar ta kama masu laifuka daban-daban 88 da masu garkuwa 10 sai kuma 'yan bindiga 20 da kuma masu fasa bututun mai 19.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Zuwa yau 28 ya watan Yuli, jami'an sojoji sun kashe 'yan ta'adda 59 tare da kama masu laifuka daban-daban 88 da masu garkuwa 10.
"Sauran sun hada da 'yan bindiga 20 da kuma masu fasa bututun mai da sacewa su 19, yayin da rundunar ta kubutar da mutane 88 daga hannun 'yan bindiga."

Gidan talabijin na Channels ta tattaro cewa rundunar ta kwace makamai 68 da kuma harsasai 1,364 dalilin wannan samame.

Sojojin sun kwato muggan makamai a hannun 'yan ta'addan

A cewar sanarwar:

"Sojoji sun kwace AK-47 guda 27 da bindigar Fiston guda biyar da sauran muggan makami daga 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sheƙa Barzahu Yayin da Suka Yi Yunƙurin Kai Hari Sansanin Sojoji a Zamfara

" Sun kuma yi nasarar kwato harsasai fiye da 1,000 da kuma kudi N41,915 da Cefa 49,000, sauran sun hada da litar bakin 323,650 da kuma litar tataccen bakin mai ba bisa ka'ida ba 128,700."

Sojoji Sun Kama Shanu 1000 Da Ke Yawo A Gonakin Jama’a Tare Da Musu Barna

A wani labarin, sojoji sun kama shanaye fiye da 1000 da suke gararanba a gonakin mutane a jihar Plateau.

Rundunar ta ce ta kama dabbobin ne a kauyen Dumunan da ke yankin Bwai a karamar hukumar Mangu da ke jihar don kawo zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel