Yan Hisbah a Jihar Kano Sun Cafke Masu Shirya Auren Jinsi a Jihar

Yan Hisbah a Jihar Kano Sun Cafke Masu Shirya Auren Jinsi a Jihar

  • Hukumar Hisbah a jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu matasa mutum biyu da ake zargi da ƙoƙarin shirya auren jinsi
  • Babban Kwamandan hukumar ya bayyana cewa an cafke matasan ne bayan bayyanar bidiyonsu suna sumbatar juna domin murnar baikon su
  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike kan matasan da ake zargi waɗanda suka musanta tuhumar da ake musu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi caraf da wasu mutum biyu da ake zargi da shirin gudanar da auren jinsi a jihar.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa babban Kwamandan Hisbah na jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shi ne ya bayyana hakan ga ƴan jaridu a ƙarshen makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Mutane Sama da 100 Kan Zargin Aika Muggan Laifuka Daban-Daban a Arewa

Hukumar Hisbah ta cafke masu shirya auren jinsi a Kano
Sheikh Daurawa ya ce ana ci gaba da bincike akan waɗanda ake zargin Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa an cafke waɗanda ake zargin ne bayan bayyanar bidiyonsu suna sumbatar juna domin murnar baikon da aka yi musu.

Shugaban na hukumar ya bayyana cewa a cikin bidiyon da hukumar ta ci karo da shi, an nuna wasu matasa mutum biyu, Khalifa da Abubakar, a wajen wani casu suna sumbatar juna, rahoton Kano Focus ya tabbatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Waɗanda ake zargin sun musanta zargin da ake musu

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun musanta zargin da ake musu, inda suka ce an shirya casun ne domin taya ɗaya daga cikinsu murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

A cewar Khalifa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, ya shirya casun ne domin taya kan shi murnar zagayowar ranar da aka haife shi ya zo duniya.

Ya yi bayanin cewa a wurin casun da ya shirya ɗin ne wani daga cikin abokansa wanda ake kira da Abubakar ya sanya masa kek a baki sannan ya ƙare da yi masa sumbata a bakinsa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Sabon Rikici Ya Ɓalle a Arewacin Najeriya, An Kashe Mutane da Yawa

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa waɗanda ake zargin su biyu suna hannun hukuma kuma za a cigaba da gudanar da bincike a kansu.

Hisbah Ta Cafke Boka a Kano

A baya rahoto ya zo cewa hukumar Hisbah a jihar Kano ta cafke wani boka da ake zargi da yi wa ɗirkawa wata matar aure ciki.

Bokan ya shiga hannun hukuma ne bayan ya yi wa matar auren ciki lokacin da ta je wajensa neman magani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng