Hisbah a jihar Kano ta kama wani bokan da ya dirkawa wata mata ciki

Hisbah a jihar Kano ta kama wani bokan da ya dirkawa wata mata ciki

  • Hisbah a jihar Kano ta kwamushe wani bata-garin boka da ya lababa ya dirkawa wata mata ciki a Dawakin Kudu
  • Matar ta ce ta je neman magani ne a wurinsa, amma ya ci amana ya ce magani ba zai yiwu ba sai ya kwanta da ita
  • Ya amsa laifinsa, ya ce wannan ba komai bane face sharrin shaidan, Hisbah na ci gaba da yin bincike a kai

Dawakin Kudu, jihar Kano - Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kwamushe wani boka da ake zargin ya lallaba, ya dirkawa wata mata ciki a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

A cewar rahoton da BBC Hausa ta tattaro, ana zargin mutumin da yiwa matar ciki ne a lokacin da ta je baran magani a wajensa.

Kara karanta wannan

Shekarunta 23: Wani Mutum Ya Wallafa Hotunansa Da Wata Mata Mai Nakasa, An ce Sun yi Aure

Muhammad Mansur, wanda mazaunin karamar hukumar Dawakin Kudu ne shi ake zargi da aikata wannan laifin, kuma an kama shi ne bayan da matar ta ce tabbas shi ya banka mata ciki.

Hisbah ta kame wani boka da ya yiwa wata mata ciki a Kano
Hisbah a jihar Kano ta kama wani bokan da ya dirkawa wata mata ciki | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Yadda lamarin ya faru kuwa shine, matar da kanta ta kai kara don neman a bi kadunta yayin da tace tana dauke da cikin watanni bakwai na boka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhammad Mansur dai fitaccen boka ne a yankinsu, kuma an ce ya yi shuhura wajen yaudarar mata ta hanyar yin lalata dasu, ciki kuwa har da matan aure.

A cewar majiya daga yankin, Muhammad na yaudarar mata ne tare da bayyana musu cewa, idan suka kwanta dashi za su samu biyan bukatar da suka kawo masa.

Manyan magungunan da ya shahara wajen badawa a cewa mazauna yankin su ne maganin mallakar miji da kuma hana kishiya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Wani Mai Hannu a Garkuwa Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya, Ya Fara Bayani

Ta kai kara gaban hukumar Hisbah, ga abin da take cewa

A cewarta, bokan ya ce matsalarta ba za ta kau ba har sai ta amince ya kwanta da ita kafin maganinta ya ci.

Ta kuma shaida cewa, bokan ya sha tunkarar saduwa da ita a lokuta mabambanta da take zuwa neman magani tare da mahaifiyarta.

Ta bayyana cewa, ya samu dama a kanta ne lokacin da ta gana dashi ita kadai, har ya shawo kanta suka aikata lalata.

Da gaske na aikata laifin, boka ya magantu

A nasa bangaren, bayan shan matsa Muhammad Mansur ya ce tabbas ya kwanta da ita, amma dai hakan ba komai bane face sharrin shaidan.

Ustaz Kabiru Musa Dawakiji, shugaban hisbah a karamar hukumar ya ce za a ci gaba da zurfafa bincike tare da daukar matakin doka yadda ya dace.

Hisbah na ci gaba da ayyuka a jihar Kano na kamo masu laifuka, a baya kunji yadda hukumar ta kame wasu da ake zargin suna luwadi.

Kara karanta wannan

Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin da Karamar Diyarsa Ta Yi Alkawarin Siya Masa Mota, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Asali: Legit.ng

Online view pixel