Hadimar Tinubu Ta Ayyana Bangaren da Gwamnatin APC Za Ta Maida Hankali a Kai

Hadimar Tinubu Ta Ayyana Bangaren da Gwamnatin APC Za Ta Maida Hankali a Kai

  • Bola Ahmed Tinubu ya na so Najeriya ta ci moriyar arzikin gas da Ubangiji ya malalawa kasar
  • Gwamnatin Najeriya za tayi amfani da sinadarin gas domin samar da wutar lantarki da ayyukan yi
  • Mai ba Tinubu shawara na musamman, Olu Verheijen ta shaida haka a wajen wani taro a Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Mai taimakawa Bola Ahmed Tinubu a kan harkokin wuta, Olu Verheijen ta ce gwamnatinsu za ta ba sha’anin gas muhimmanci sosai.

Misis Olu Verheijen ta gabatar da jawabi a sakatariyar “Decade of Gas” da ke garin Abuja, a nan ta yi wannan bayani, Premium Times ta kawo rahoton.

Gwamnatin tarayya ta fito da wannan tsari na “Decade of Gas” domin ganin cewa gas ya zama babban makamashin samun wuta a gidaje da kamfanoni.

Kara karanta wannan

Ja Ya Faɗo-Ja Ya Ɗauka: ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Amince a Kashe Masu N70bn

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Gas zai zama ruwan dare?

A cewar Verheijen, Mai girma shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba gas muhimmancin gaske, kuma zai so kasar ta ci moriyar wannan arziki da ta mallaka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai ba shugaban kasar shawara ta ce ana burin Najeriya za ta tashi daga kasar da ta ke fitar da gas din LNG, a koma ana amfani da shi sosai a kamfanoni.

Hukumar dillacin labarai ta kasa (NAN) ta ce wannan tsari da aka fito da shi ya fara aiki a 2021, kuma ana sa ran cin ma na nasara nan da shekarar 2030.

Gudumuwar da NMDPRA za ta bada

An rahoto shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed ya na cewa gwamnati na kokarin ganin kowa ya koma amfani da gas bayan fita da shi zuwa waje.

Farouk Ahmed ya ce a baya kamfanin Shell aka bari da dawainiyar gas a Najeriya, wannan karo kuwa an kafa sakatariya wanda NMDPRA za ta rika sa ido.

Kara karanta wannan

Sakataren APC Ya Jero Irin Mutanen da Shugaban Kasa Zai Dauko Su Zama Ministoci

Sakatariyar aikin gas din ya na unguwar Jabi a Abuja a karkashin jagorancin Ed Ebong.

Kamar yadda mu ka samur rahoto, Daily Post ta ce Ed Ebong ya yi bayanin kokarin da ake yi wajen fito da tsare-tsare domin ganin an amfana da albarkatun.

Muddin ba a fara samar da bututu ba, Mista Ebong ya ce gas ba zai kai wuraren da ake bukata ba.

Za a dauko Minista daga LP

An rahoto cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana so ya jawo cikas a bangaren jam’iyyar LP ta hanyar nada wani a cikinsu a matsayin Minista a gwamnati.

Maganar Daniel Bwala ta jawo hasashen mutane ya karkata ga Pat Utomi da Dr. Doyin Okupe wanda su na cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng