'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Tara a Wani Sabon Hari a Jihar Plateau

'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Tara a Wani Sabon Hari a Jihar Plateau

  • Ƴan bindiga sun sake kai mummunan hari a jihar Plateau inda suka salwantar da rayukan bayin Allah da dama
  • Ƴan bindigan sun kai farmakin ne cikin tsakar dare a ƙauyen Sabon Gari na ƙaramar hukumar Mangu ta jihar
  • A yayin harin ƴan bindigan sun halaka mutum da ƙona gidaje shida kafin zuwan jami'an tsaro su taka musu burki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun halaka mutum tara da ƙona gidaje shida a ƙauyen Sabon Gari cikin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Mr Jerry Datim, ɗaya daga cikin shugabannin ƙauyen shi ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a birnin Jos ranar Lahadi.

Yan bindiga sun kai sabon hari a jihar Plateau
'Yan bindigan sun halaka mutum da kona gidaje Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Datim, wanda shine shugaban ƙungiyar Global Society for Middle Belt Heritage na ƙasa, ya bayyana cewa an kai harin ne a ranar Asabar da daddare, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

"Kuskure Ne Babba": Tsohon Mataimakin Sufetan 'Yan Sanda Ya Ankarar Da Tinubu Kan Illar Shawarar Yarima Ta a Yi Sulhu Da 'Yan Bindiga

"Jiya da daddare, ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen mu, Sabon Gari cikin ƙaramar hukumar Mangu, sun ƙona gidaje shida da lalata kayayyaki masu yawa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya zuwa yanzu mun samu gawarwarki tara, muna ci gaba da dubawa saboda har yanzu wasu mutanen ba a san inda su ke ba."

Ya yabawa jami'an tsaro bisa ɗaukin da suka kawo

Sai dai, Datim, ya yabawa jami'an tsaron Operation Rainbow, wasu jami'an tsaro da ke a jihar kan yadda suka kawo ɗauki bayan an kai harin.

"Ina son na yabawa jami'an operation rainbow, ɗauki da suka kawo ya sanya abubuwa sun daidaita."
"Muna kira ga gwamnati da ta mara musu baya ta hanyar samar musu da kayan aiki domin kawo ɗauki akan lokaci.

Da aka tambaye shi ko mutanen ƙauyen sun gudu, Datim ya bayyana cewa sun yanke shawarar tsayawa su kare martabar garinsu na kaka da kakanni, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Yi Wa Shugaba Tinubu Tonon Silili Kan Dalilin Da Ya Sanya Yake Nade-Naden Mukamai

Jami'an tsaro sun tabbatar da aukuwar harin

Kyaftin James Oya, kakakin rundunar Operation Safe Haven (OPSH) ta sojojin Najeriya, ya tabbatar da aukuwar harin.

Oya, wanda bai tabbatar da yawan mutanen da aka kashe ba, ya bayyana cewa kwamandan rundunar, Manjo Janar Abdusalam Abubakar, ya jagoranci sojoji zuwa ƙauyen.

Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Bindiga a Jihar Zamfara

A wani labarin kuma, jajirtattun dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar tura wasu ƴan bindiga inda ba a dawowa a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun kuma ceto mutum 24 da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su a yayin sumamen da suka kai a maɓoyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng