Bidiyon Dala: 'Binciken Kimiyya Ya Yi Wa Ganduje Fallasa,' Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano

Bidiyon Dala: 'Binciken Kimiyya Ya Yi Wa Ganduje Fallasa,' Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta sanar da sakamakon bincikenta a kan bidiyon dala na Abdullahi Umar Ganduje
  • Hukumar PCACC ta tabbatar ingancin bidiyon kamar yadda ta ce sakamakon binciken Kimiyya ya gano cewa bidiyon ba na bogi bane
  • Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ne ya tabbatar da sahihancin bidiyon a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano (PCACC) ta ce binciken kimiyya ya tabbatar da cewar bidiyon dala na tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba na bogi bane.

A shekarar 2017 ne Daliy Nigerian, wata jaridar yanar gizo ta saki wasu bidiyoyin Ganduje wanda ake zargin yana ta karbar cin hanci daga wajen yan kwangila.

Gwamna Abba Kabir Yusuf da Tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Bidiyon Dala: 'Binciken Kimiyya Ya Yi Wa Ganduje Fallasa,' Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf, Abdulahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Bincike ya tabbatar da bindiyon gaskiya ne, Rimingado

Kara karanta wannan

Bidiyon Dala: Hukumar Yaƙi Da Rashawa ta Kano Ta Bayyana Yadda Bidiyon Ya Taba Ƙimar Kano a Idon Duniya

Sai dai da yake magana a wani taron tattaunawa kan yaki da rashawa a Kano a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya tabbatar da sahihancin bidiyoyin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rimingado ya ce tun bayan sakin bidiyoyin, mutane na ta kalubalantarsa da ya tabbatar da ko tsohon gwamnan ba shi da laifi ko akasin haka kan lamarin, rahoton Daily Trust.

Ya kara da cewar hukumarsa ta fara bincike a 2018 amma bata yi nisa ba saboda Ganduje, wanda ya kasance gwamna a wancan lokacin yana da rigar kariya.

Gwamnatin Kano ta kaddamar da bincike kan bidiyon dalar Ganduje

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta kaddamar da bincike a hukumance kan tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, kan faifan bidiyonsa na karbar rashawa.

Kara karanta wannan

Wata Kungiya Ta Nemi a Gudanar Da Bincike Na Gaggawa Kan Yadda Gwamnan Zamfara Dauda Lawal Ya Tara Dukiyarsa

Shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimingado ne ya bayyana hakan ranar Talata, 4 ga watan Yuli yayin wata ganawa da manema labarai a Kano.

A makon jiya ne shugaban hukumar ya sha alwashin sake farfado da bincike kan bidiyon tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

An kama tsohon kwamishinan Ganduje kan badakalar naira biliyan 1

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa an kama tsohon kwamishinan tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan badakalar naira biliyan daya, jaridar Aminiya ta rahoto.

Shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar da aka dawo da shi, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya yi alkawarin cewa duk wadanda ake zargi da aikata cin hanci da rashawa sai sun biya bashin abubuwan da suka aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng