Farashin Fetur Ya Sauko Saboda Rashin Ciniki, Ana Tsakar Rade-Radin Ƙara Tsada

Farashin Fetur Ya Sauko Saboda Rashin Ciniki, Ana Tsakar Rade-Radin Ƙara Tsada

  • Wani jagora a IPMAN ya shaida cewa in ban da a tashoshin NNPCL, farashin man fetur ya canza
  • Abubakar Maigandi ya nuna an samu raguwar akalla N5 a kan kowace lita a tashohin ‘yan kasuwa
  • Mataimakin shugaban kungiyar ta IPMAN ya alakanta hakan da karancin kudi a hannun mutane

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - ‘Yan kasuwa sun karya farashin man fetur a tashoshinsu a karshen makon nan, dalilin kuwa shi ne saboda samun kasuwa domin ciniki ya ragu.

The Nation ta samu labari cewa farashin man fetur ya sauka a tasoshin ‘yan kasuwa. Farashin lita ya sauka daga N502 ko N503 zuwa tsakanin N495 – N496.

Amma farashin bai canza a tashoshin kamfanin NNPCL ba, litar fetur ta na nan a kan N479.6.

Farashin Fetur
Tankokin man fetur Hoto: AFP/ANNE-CHRISTINE POUJOULAT
Asali: AFP

Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwan mai a Najeriya, Alhaji Abubakar Maigandi ne ya fara bayyana halin da ake ciki a tashoshin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fitaccen malamin addini a Najeriya ya fadi a filin jirgin sama saboda tsananin rashin lafiya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kasuwa ta fara ja baya?

Abubakar Maigandi ya shaidawa jaridar cewa su na tunanin raguwar amfani da fetur da ake yi ya jawo rashin ciniki, hakan ya yi dalilin saukar farashi.

‘Dan kasuwan yake cewa wadanda su ka saba sayen fetur musamman ma’aikatan gwamnati sun shiga halin wayyo Allah a dalilin janye tallafi da aka yi.

“Su na rage farashin idan aka kamanta da yadda da su ka saida shi a makon jiya. Su na saida lita tsakanin N495 ko N496, bayan ya kai N502 ko N503
A Legas, farashin da ake saidawa kenan a mafi yawan tashoshin, kamfanin NNPC na gwamnati su na cigaba da saida lita a kan tsohon farashi na N479.6.

- Abubakar Maigandi

Ana tsoron farashi zai tashi

Maigandi ya kuma nuna cewa ya kamata a shigo da sabon fetur idan ba haka ba mai zai kare, a cewarsa rabon da a kawo mai tun kafin janye tallafi a Mayu.

Kara karanta wannan

Kungiyar IPMAN Ta Yi Karin Haske a Kan Yiwuwar Litar Man Fetur Ya Koma N700

Legit.ng Hausa ta fahimci hakan ya faru ne a lokacin da ake yada labarai cewa litar mai zai karu daga kimanin N540 zuwa abin da zai iy akai N700 a yanzu.

Mun samu rahoto cewa mutane sun yi ta cincirindo zuwa gidajen mai domin tanadin fetur da za su yi amfani da shi saboda tsoron farashin ya sake tashi sama.

Farashi ba zai tashi ba - IPMAN

Wani 'dan kasuwa ya fito kwanaki yana hasashen cewa daga N540 fetur zai koma akalla N700 a yankin Arewa, ya ce za a dawo sayen lita kan N600 a Legas.

An rahoto shi yana cewa abin da ya ke gani shi ne mutanen da ke Legas za su biya kusan N600, mutanen Arewa za su rika sayen duk lita a kan fiye da N700.

Asali: Legit.ng

Online view pixel