Dalla-dalla kan sabon nisabin sadaki tare da Sheikh Khamis Al-Misriy

Dalla-dalla kan sabon nisabin sadaki tare da Sheikh Khamis Al-Misriy

- Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta bayyana N22,094 a matsayin karancin sadaki a shekarar nan

- Kamar yadda Sheikh Khamis Al-Misriy yayi karin haske, yace ba a biyan kasa da hakan kenan sai dai sama da haka

- Malamin ya kara da cewa ba a yafe sadaki, sai dai matar da za a aura na iya yi wa mijin da za ta aura rangwame

A makon nan ne majalisar koli ta addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bayyana nisabin karancin sadaki a kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta samu zantawa da Sheikh Khamis Al-Misriy, limamin masallacin Abu Ubaidah Bn Jarrah dake bye-pass jihar Kaduna domin samun karin haske.

Kamar yadda malamin ya sanar, nisabi dai shine wani ma'auni da ake gwadawa domin a gane darajar kudi da inda ya kai. A musulunce kuwa ana kiran shi da kaso daya bisa hudu na dinari daya.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun yi wa makiyaya 22 kisan gilla a garin Monguno dake Borno

Dalla-dalla kan sabon nisabin sadaki tare da Sheikh Khamis Al-Misriy
Dalla-dalla kan sabon nisabin sadaki tare da Sheikh Khamis Al-Misriy
Asali: Original

KU KARANTA: Darikar Tijjaniya ta musanta baiwa Muhammadu Sanusi II shugabanta na Najeriya

Kamar yadda malamain ya sanar, nisabi yana da alaka da tashi ko saukar kudade masu daraja a duniya kamarsu dala, euro da sauransu.

"Da nisabi ake auna karancin sadaki na diya mace ko kuma yanke hannun wanda yayi sata," cewar malamin.

Kamar yadda Shehin malamin yace, mutum ba zai iya biyan sadaki kasa da N22,094, amma zai iya biyan sama da hakan.

A yayin da Legit.ng ta tambaya malamin zamanin Manzo Allah da ake bada kissar matan da ke cewa sun yafe sadaki, ko kuma haddar Al-Qur'ani mai girma suke so, sai yace:

"Sadaki ba a hakura da shi. Komai karantarsa ana badawa. Amma tunda mace ce ake baiwa sadakin, tana da damar yin rangwame. A maimakon a bada N22,094, za ta iya cewa tayi rangwame a bada N10,000 ko N5,000."

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami darakta janar na hukumar binciken yanayi (NiMet), Farfesa Sani Mashi.

Wa'adin Mashi zai cika ne a watan Janairun 2022 amma shugaban kasa ya maye gurbinsa da Bako Mansur Matazu.

Matazu yana da digirin digirgir a fannin Geography kuma mamba ne a kungiyoyi kamar haka: Nigerian Environmental Society, African Forestry Forum, Nigerian Meteorological Society, the Climate Change Network, Nigeria and the renewable Energy and Energy Efficiency, Nigeria (REEN).

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: