"Ina Son Mijina Duk da Yana Duka Na Kamar Jaka" Mata Ta Fada Wa Kotu a Kaduna

"Ina Son Mijina Duk da Yana Duka Na Kamar Jaka" Mata Ta Fada Wa Kotu a Kaduna

  • Wata mata, Maryam Musa, Ata kai karar Mijinta gaban Kotun shari'a mai zama a Magajin Gari Kaduna kan cin mutunci da wulakanci
  • Ta roki Kotun ta raba auren matuƙar mijin ba zai daina dukanta ba amma tace tana kunarsa har yanzu
  • Magidancin mai suna Kabiru Sulaiman ya musanta zargin sahibarsa, ya roki Kotu ta ba shi lokaci ya sulhunta tsakaninsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - Wata matar aure mai suna Maryam Musa ta kai karar mijinta, Kabiru Sulaiman gaban Kotun shari'ar Musulunci mai zama a Magajin Gari Kaduna.

Matar ta shigar da ƙarar abokin rayuwarta ne kan wulaƙanci da cin mutuncin da yake mata, kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.

Kotun shari'ar Musulunci.
"Ina Son Mijina Duk da Yana Duka Na Kamar Jaka" Mata Ta Fada Wa Kotu a Kaduna Hoto: Shari'a Lawa
Asali: Facebook

A rahoton da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattara, Maryam ta shaida wa Kotu cewa Kabiru ya ci mata mutunci kuma ya kore ta daga gidansa bayan sun ɗan samu saɓani.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Daba Suka Caccaki Wani Dan Kasuwa Har Lahra a Jihar Kano

"Ya sa hannunsa ya shaƙo ni sannan ya naushe ni a ciki, kuma ya fatattake ni daga cikin gidansa. Har yanzu ina ƙaunar habibi na amma dukan da yake mun ya yi yawa."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Idan har ba zai iya daina duka na kamar jaka ba, to kawai ya sawwake mun, Allah ya haɗa kowa da rabonta," inji Maryam.

Shin magidanci ya amsa laifin matarsa take masa a gaban Kotu?

Da yake kare kansa a zaman Kotu ta bakin lauyansa, Malam Jamilu Sulaiman, mijin matar ya musanta dukkan zarge-zargen da mai ɗakinsa take masa.

Ya shaida wa alkalin kotun shari'a cewa ko kaɗan ba halinsa bane dukan matarsa da suka yi auren soyayya.

Ya kuma roki Kotun ta taimaka masa ta ba shi wani ɗan lokaci domin ya rarrashi matarsa su yi sulhu a gida don a samu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Dirama a Kotu: Wata Matar Aure Maryam Ta Nemi a Raba Aurenta da Mijinta Saboda Rashin Kulawa

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Bayan sauraron kowane ɓangare alkalin Kotun, mai shari'a Malam Isiyaku Abdulrahman, Ya ɗage zaman zuwa 10 ga watan Yuli domin ba su dama su yi sulhu.

"Ba Zan Karɓa Ba Sai Kin Duƙa" Miji Ya Umarci Matarsa a Bidiyo, Ya Ki Karban Abinci

A wani rahoton na daban kuma Wata mata 'yar Najeriya ta sha mamaki yayin da habibinta ya umarci ta duƙa kan guiwa kafin ya karɓi abincin da ta kawo masa.

Magidancin ya gaya mata cewa shi ɗan gargajiya ne kuma ya zama dole ta duƙa kan guiwowinta idan zata ba shi abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel