Ba Zamu Nemi Shulhu da Shugabannin 'Yan Bindiga Ba, Gwamnatin Zamfara

Ba Zamu Nemi Shulhu da Shugabannin 'Yan Bindiga Ba, Gwamnatin Zamfara

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ko kaɗan ba zata nemi sulhu da yan bindiga ba, ta ce wanda aka yi a baya bai ɓulle ba
  • Sakataren gwamnati, Alhaji Abubakar Nakwada, ya ce maimakon haka gwamnatinsu zata yi kokarin lalubo 'yan ta'adda ta murƙushe su
  • Ya kuma sanar da al'umma cewa daga yanzu sabuwar gwamnati ta soke duk wani fili da aka sayar wa wani ko kamfani

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ranar Talata ta ce ba zata taɓa rungumar tattaunawar zaman lafiya ko jawo wasu hatsabiban yan bindiga a yi sulhu a jihar ba.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Nakwada, shi ne ya bayyana haka yayin zantawa da 'yan jarida a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Taswirar jihar Zamfara.
Ba Zamu Nemi Shulhu da Shugabannin 'Yan Bindiga Ba, Gwamnatin Zamfara Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ya ce sabuwar gwamnatin Dauda Lawal ba ta da niyyar zama da wani shugaban 'yan bindiga ko wakilinsu da nufin tattaunawar neman zaman lafiya, Dailypost ta rahoto.

Kara karanta wannan

An Yi Matukar Farin Ciki Yayin Da Aka Biya Ma'aikatan Jihar Arewa Albashi Bayan Shafe Watanni 7 Ba Ko Sisi

Ta wace hanyar sabuwar gwamnatin Zamfara zata yi kokarin dawo da zaman lafiya?

Nakwada ya ƙara da bayyana cewa wannan gwamnatin mai ci ta shirya tsaf, mai makon tattaunawa da yan bindiga, ta zaɓi zakulo su duk inda suka ɓuya a murƙushe su harda masu ɗaukar nauyinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar zata yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa yaƙin da ake da ta'addanci ya kai ga nasara.

Zamu kwato duk abinda fsohuwar gwamnatin Matawalle ya sace

Bugu da ƙari, SSG na jihar Zamfara ya zargi tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle da ɗibar biliyoyin kuɗaɗe wajen aiwatar da ayyukan alfarma da ba su da wani tasiri a rayuwar talaka.

"Gwamnatin Matawalle ta kashe biliyan N10bn wajen siyo motoci kuma ba ta aje wani bayanin da zai tabbatar da haka ba. Alhali muƙarraban gwamnati ne suka yi kashe mu raba da wasu motocin."

Kara karanta wannan

Zargin Batanci: Gwamnatin Sokoto Ta Bayyana Irin Matakin Da Za Ta Dauka Kan Masu Batanci Ga Annabi (SAW)

"Gwamnatin mu tana amfani da wannan damar wajen sanar da ɗaukacin mazauna Zamfara cewa mun kwace duk wasu filaye da aka cefatar wa shafaffu da mai ko wasu kamfanoni."

- Alhaji Abubakar Nakwada.

Shugaba Tinubu Ya Gana da Tinubu a Birnin Landan

A wani rahoton na daban kuma Kafin dawowa gida Najeriya, Shugaba Tinubu ya gana da magabacinsa, Muhammadu Buhari a Landan na kasar Burtaniya.

Har yanzu babu cikakken bayani kan abinda manyan jiga-jigan biyu suka tattauna amma Hoton ganawarsu ya karaɗe soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel