Matashi Ya Zama Mai Gidan Kansa, Ya Dankara Gini Mai Kyau Tare Da Zuba Kujerun Waje

Matashi Ya Zama Mai Gidan Kansa, Ya Dankara Gini Mai Kyau Tare Da Zuba Kujerun Waje

  • Wani matashi dan Najeriya ya zuba jari a rayuwarsa inda ya gina hadadden gida mai cike da kayan alatu
  • Da yake baje kolin gidan TikTok, mutane da dama sun sha mamakin haduwar cikin gidan da kuma sabbin kujeru da aka zuba
  • An gano mutumin yana gyara wurare yayin da ake shigo da kayan wuta cikin gidan

Wani matashin miloniya ya kerawa kansa hadadden gida bayan ya tara abun duniya. Mutumin ya wallafa bidiyon da ke hasko gidan a TikTok.

Bayan an yiwa koina fenti, matashin (@user4947622742412) ya kashe kudi sosai wajen siyan kayan amfanin gida masu inganci. Wani bangare na gidan na da hadadden bango da fitilun alfarma.

Matashi da hadadden gida
Matashi Ya Zama Mai Gidan Kansa, Ya Dankara Gini Mai Kyau Tare Da Zuba Kujerun Waje Hoto: @user4947622742412
Asali: TikTok

Hadaddun kujeru, komai sabbi a gidan

Gaba daya kujerunsa an shigo da su ne daga waje kuma lullube suke da ledoji. Miloniyan ya ce zai yi bikin bude gidan a ranar Lahadi, 25 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

“Yallabai Baka Da Kunya”: Matashi Ya Dauki Mahaifinsa Dan Tsurut a Kafada, Bidiyon Ya Yadu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutane da dama sun yi tururuwan zuwa sashin sharhi na bidiyon dauke da sakonnin taya murna.

A wani bidiyon, ya kasance dauke da kwalayen kayayyakin gida a bakin kofarsa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

princepabloak ya ce:

"Na tayaka murna maigida Allah ya zai albarkaceka don ka siya filin da ke kusa da kai domin ka fadada shi."

Happy ness :

"Na tayaka murna mai gida. Ya kamata ace injiniyanka ya yi kofar shiga gidan daga hannun dama saboda motarka amma duk ya yi."

Edo Garçon ya ce:

"Karin nasara sarki Allah zai yi maka fiye da haka amin."

RightMan ya ce:

"Aiki mai kyau, na so ace kana da isasshen fili, karin nasara a gareka."

saintkizz0 ya ce:

"Na taya ka murna dan uwa. ka mallaki gida mai kyau a nan."

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Cafke Kasurgumin Dan Fashi Kwanaki 3 Da Sakinsa Daga Yari

Tomato ta ce:

"Na tayaka murna dan uwa, amma babu fili a gidan kuma."

Matashi ya nunawa duniya mahaifinsa dan tsurut, ya ce yana alfahari da kasancewarsa ubansa

A wani labari na daban, wani matashi ya yi fice a soshiyal midiya bayan ya jinjinawa mahaifinsa wanda ke da karamin jiki.

Matashin wanda ke amfani da suna @walmart1805 a TikTok ya wallafa bidiyon mahaifinsa a ranar iyaye maza na duniya kuma nan take bidiyon ya yadu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel