“Ya Fi Kudin Jini”: Matashiya Ta Yarda Ta Mari Mahaifiyarta a Kan Miliyan N2

“Ya Fi Kudin Jini”: Matashiya Ta Yarda Ta Mari Mahaifiyarta a Kan Miliyan N2

  • Wani bidiyo da ya yadu na budurwa da ta ce za ta iya marin mahaifiyarta ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • A bidiyon da ya yadu, wani mutum ya tambayi budurwar kan ko za ta yarda a bata miliyan 2 don ta mari mahaifiyarta
  • Abun mamaki, ta yarda da bukatar harma ta yi alkawarin karawa a kan aikin idan aka biya ta kudin kamar yadda aka yi alkawari

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jama'a sun yi cece-kuce bayan wani bidiyo na matashiya da ta yarda ta mari mahaifiyarta ya bayyana a dandalin TikTok.

Matashiyar budurwar ta bayyana ra'ayinta cike da karfin gwiwa bayan an bukaci ta mari mahaifiyarta kan naira miliyan 2.

Matashiya na magana
“Ya Fi Kudin Jini”: Matashiya Ta Yarda Ta Mari Mahaifiyarta a Kan Miliyan N2 Hoto: @kikiotolu/TikTok.
Asali: TikTok

Tambayar ta bugeta sosai amma hakan bai sa ta karaya ba. Ta yi dariya da farko kafin ta bayar da amsarta cike da karfin gwiwa.

Kara karanta wannan

"Bayan Wuya": Matashiya Wacce Ke Yawon Talla Ta Koma Turai, Ta Fara Aiki a Matsayin Malamar Asibiti

A cewarta, za ta mari mahaifiyarta a kan wannan makudan kudaden. Ta yi bayanin cewa mahaifiyar tata za ta fahimci lamarin kuma ba za ta dauki abun a zuciya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da take kare kanta, ta bayyana cewa tunda dai bata yi amfani da mahaifiyar tata wajen asiri (kudin jini) ba, toh mahaifiyar za ta karbi kudin a madadin marin.

Ta kara da cewar za ta yarda ta mari mahaifiyar tata sau 10 domin a kara mata kudaden.

Jama'a sun yi martani

@IJOBA101 ya tambaya:

"Wani karni na biyo duniyan nan?"

@Bleazy's invention ya ce:

"Ta yi kama da zazuu sosai."

@Oyinkanslim12 ya rubuta:

"Tunda ba kudin jini na yi da ita ba."

@Mimi T. ta yi ihu:

"Fahimci me?!"

@Taiwo Aj ta yi martani:

"Uwata?! Ba zan iya ba faaaa tamkar uwargiyata ce."

@rosa ta yi martani:

Kara karanta wannan

“Manta Don Kin Ganni a Kan Babur”: Dan Najeriya Ya Tsara Budurwa a Kan Babur, Bidiyon Ya Yadu

"Watakila mahaifiyarta na da sanyi."

@Naeyomie Campbell ta ce:

"Ba zan taba iyawa ba, ko a kan miliyan 10, uwargiyata a duniya."

@Wumzy Nilsa ya ce:

"Yarinya mara hankali."

Kalli bidiyon a kasa:

Bayan hade asusun banki suna tara kudi da mijinta, mata ta fece da kudaden

A wani labari na daban, wata matar aure ta yi nasarar yashe gaba daya kudin da ke cikin asusun hadin gwiwa nata da na mijinta.

Matar ta kuma yi batan dabo bayan ta kwashe kudin amma sai taki rashin sa'a domin dai an kama ta daga bisani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel