Kano: NDLEA Ta Kwamushe Mutum 1,064 Kan Zargin Ta'ammali Da Kwayoyi

Kano: NDLEA Ta Kwamushe Mutum 1,064 Kan Zargin Ta'ammali Da Kwayoyi

  • Hukumar NDLEA a jihar Kano ta ce ta kama wadanda ake zargi da ta'ammali da kwayoyi mutum 1,064 a jihar
  • Kakakin rikon kwarya na hukumar, Sadik Maigatari shi ya bayyana haka a ranar Asabar 24 ga watan Yuni a Kano
  • Hukumar ta ce ta kuma yi nasarar kwace tan 7.5 na miyagun kwayoyi da suka hada da tabar wiwi da hodar iblis da sauransu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Hukumar Yaki, Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Kano ta ce ta kama tan 7.5 na miyagun kwayoyi a jihar.

Hukumar har ila yau, ta ce ta kama masu alaka da miyagun kwayoyin mutum 1,064 tsakanin watan Yuni na 2022 zuwa watan Yuni na wannan shekara.

Jami'an Hukumar NDLEA a Najeriya
Jami'an NDLEA sun kama wadanda ake zargi da ta'amulli da kwayoyi a Kano. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

“Ya Fi Karfin Talaka”: Jami’ar Najeriya Ta Kara Kudin Makaranta Da Kaso 300, Dalibai Sun Yi Martani

Kakakin rikon kwarya na kungiyar, Sadik Maigatari shi ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Asabar 24 ga watan Yuni a Kano.

Ya bayyana matsalar miyagun kwayoyi a Kano abin takaici

Ya ce matsalar sha da safarar miyagun kwayoyi abu ne da ke kawo cikas a lafiya da rayuwar al'umma gaba daya, Punch ta tattaro.

Ya kara da cewa cikin wadanda aka kama akwai mata 63 da maza 1,001 wanda aka kama da miyagun kwayoyin da suka hada da tabar wiwi da hodar iblis da sauransu.

Maigatari ya ce tsawon wannan lokaci an yi nasarar hukunta wadanda ake zargi 111, yayin da 126 ke kotu, The Nation ta tattaro.

Ya godewa Shugaban NDLEA bisa goyon baya da yake ba su

Ya godewa shugaban hukumar, Janar Buba Marwa mai ritaya, inda ya ce irin hadin kan da yake ba su shi ne dalilin nasarar da suke samu, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Abuja: Za Mu Kwace Shanu Mu Kuma Kama Duk Wanda Ke Kiwonsu A Tituna - FCTA

A cewarsa:

"Muna yabawa gwamnatin jihar Kano, da shugabannin kananan hukumomin Rano da Tudun Wada da kuma Sarkin Rano da kungiyoyi masu zaman kansu da jami'an tsaro.
"Muna aiki ba dare ba rana, dole mu hada karfi don ganin mun dakile wannan matsala da ta addabi duniya baki daya.
"Za mu ci gaba da kamawa da kuma gurfanar da su a gaban kotu, amma za mu mutunta su kamar yadda ya dace.
"A yau 'Ranar Kwaya ta Duniya' ya kamata mu dage don hana nuna wariya ga masu ta'ammali da kwaya da kuma kula da kariyar lafiyar al'umma."

NDLEA Ta Yi Kama Wasu Rikakkun Masu Safarar Miyagun Kwayoyi a Legas

A wani labarin, Hukumar Hana Sha da Fataucin Kwayoyi (NDLEA) ta kama wasu wadanda ake zargi da safarar kwayoyi a Lagos.

An kama wadanda ake zargin ne a filin jiragen saman Murtala Mohammed da miyagun kwayoyi a birnin Lagos.

Kara karanta wannan

NLC Ta Yi Gargadi Kan Shirin Kara Kudin Wutar Lantarki A Najeriya, Ta Bayyana Matsayarta

Draktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 18 ga watan Yuni inda ya ce wadanda aka kaman sun hada da Nnamdi Eyah da UgwuoKE Oluchukwu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel