Hukumar Jarrabawar JAMB Ta Ce Dalibai Za Su Fara Rubuta Jarrabawa Ta Hanyar Amfani da Wayar Hannu

Hukumar Jarrabawar JAMB Ta Ce Dalibai Za Su Fara Rubuta Jarrabawa Ta Hanyar Amfani da Wayar Hannu

  • Hukumar shirya jarrabawa ta JAMB ta bayyana cewa, za ta fara ba dalibai damar zuwa cibiyoyin jarrabawa da wayoyin hannu
  • Wannan zai taimaka wajen tabbatar da an yi jarrabawar da za ta rahe kashe kudi daga hukumar ta JAMB
  • Ana yawan samun sauye-sauye da ci gaba a hukumar shirya jarrabawar shiga jami'a a Najeriya, musamman a wadannan shekarun

FCT, Abuja - Hukumar shirya jarrabawa ta JAMB ta bayyana cewa, za ta fara barin masu rubuta jarrabawar UTME da DE su yi amfani da wayoyin hannunsu.

Wannan na zuwa ne daga bakin magatakardar hukumar, farfesa Ishaq Oloyede, inda ya ayyana shirin na JAMB da ‘Bring Your Own Device’.

Ya bayyana cewa, hakan zai rage adadin kudade da hukumar ke kashewa wajen gudanar jarrabawar a duk wata shekara.

Kara karanta wannan

An Maido Da Shugaban Leken Asiri da Buhari Ya Kora Daga Aiki? Hukumar NIA Ta Fayyace Gaskiyar Lamari

JAMB ta kawo tsarin ba dalibai damar amfani da wayar hannu wajen rubuta jarrabawar UTME da DE
Hukumar shirya jarrabawa ta JAMB | Hoto: Joint Admission and Matriculation Board (JAMB)
Asali: Facebook

Manufar yin wannan sauyi

Oloyede ya bayyana haka ne a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni a taron manufofin hukumar na 2023 da ke gudana a Cibiyar Shari’a ta Kasa a Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

“A batun ci gaba, muna duban kawo BOYD – umarni ga daliban JAMB su rika zuwa da wayoyinsu. Zai rage kashe kudade amma ba zai taimaka wa ilimin zamani, za a kafa kotun hukunta masu aikata laifukan satar amsa a jarrabawa ta wayar hannu yayin da cibiyoyi kuma za su magance lamarin rashin bin ka’ida."

Hakazalika, ya ce hukumar za ta yi hadin gwiwa da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsakin da suka dace don tabbatar da ba a samu matsala ba a shirin.

Ba wannan ne karon farko da hukumar JAMB ke zuwa da sauye-sauye ba, takan bayyana sauyi a ka'idojin rubuta jarrabawa a lokuta mabambanta.

Kara karanta wannan

Fitaccen Mamban APC Ya Magantu Kan Sauya Shekar Tsohon Gwamnan PDP Zuwa APC

JAMB ta sanar da sabon makin shiga, Poly da FCE

A bangare guda, hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta fitar da sabon mafi karancin maki (Cut of mark) na shiga manyan makarantu a zangon 2022/2023.

Daily Trust ta rahoto cewa JAMB ta amince da maki 140 zuwa sama a matsayin mafi karancin makin neman gurbin shiga jami'o'in Najeriya a zangon karatu 2022/2023.

Shugaban JAMB na ƙasa, Farfesa Is-haq Oloyede, ne ya faɗi haka yayin da yake jawabi kan neman gurbin shiga makarantun gaba da Sakandire a wurin taron tsare-tsaren 2023 a Abuja ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel