Kano: Ganduje Ya Ce Sake Binciken Bidiyon Dala Da Ake Shirin Yi Ko A Jikinsa, Ya Bayyana Matakin Da Zai Dauka

Kano: Ganduje Ya Ce Sake Binciken Bidiyon Dala Da Ake Shirin Yi Ko A Jikinsa, Ya Bayyana Matakin Da Zai Dauka

  • Tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana binciken bidiyon dala da ake shirin yi ko a jikinsa
  • Gwamnan na magana ne akan zargin karbar rashawa da aka gano a wani faifan bidiyon da aka wallafa a shekarar 2019
  • Kwamishinan tsohon gwamnan, Muhammad Garba ya ce batun wannan faifan bidiyo ko kadan bai damesu ba

Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana matakin da gwamnatin jihar take shirin dauka akansa na ci gaba da binciken bidiyon dala ko a jikinsa.

Gwamnan na magana ne akan bidiyon dala da aka gano shi a ciki yana karbar rashawa wanda wata gidan jarida ta wallafa a 2019.

Shirin sake binciken bidiyon dala da gwamnatin Kano ke yi ko a jikina, Ganduje
Tsohon Gwamna Ganduje Da Shugaban Yaki Da Rahawa, Muhuyi Rimingado. Hoto: Legit Hausa.
Asali: Facebook

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a jihar, Magaji Muhuyi Rimingado ya sha alwashin ci gaba da bincike akan faifan bidiyon dama sauran korafe-korafe akan tsohon gwamnan.

Kara karanta wannan

“Aiki Ya Yi Kyau”: Matashi Ya Kammala Hadadden Gidansa, Ya Zuba Kujeru Yan Waje Da Kayan Alatu

Muhuyi ya ce bayan bidiyon dala akwai korafe-korafe da dama akan Ganduje

Rimingado wanda tsohon Gwamna Ganduje ya tube shi daga mukaminsa, ana zargin ya tube shi ne saboda binciken da yake yi akan wasu kwangiloli da ake tunanin Ganduje ya bai wa iyalansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhuyi Magaji ya kara da cewa bayan haka, akwai zarge-zarge akan kudade da suka shafi kananan hukumomin jihar da kuma na haraji, BBC Hausa ta tattaro.

Ganduje ta bakin tsohon kwamishinan yada labaransa, Muhammad Garba ya bayyana cewa hakan ko kadan bai dame su ba kuma ko a jikinsu, cewar Daily Trust.

Ganduje ya ce magana ce ta kotu ba shirme ba

A cewarsa:

"Magana ce ta shari'a, Muhuyi a matsayinsa na lauya ya fi kowa sanin me ya kamata ya yi, za mu zuba ido mu ga abin da zai yi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dala: Rimingado Ya Sha Alwashin Cigaba Da Bincikar Ganduje Bayan Abba Gida Gida Ya Dawo Da Shi Kan Mukaminsa

"Yana da dama ya binciki maganar da ke kotu tun da ya fi kowa sani, idan kuma babu dama, nan ma ya fi kowa sani.
"Na yi magana da Ganduje abun bai dame shi ba ko kadan, saboda lamari ne na shari'a."

Ya bayyana duk lokacin da hukumar ta gayyaci Ganduje, sai ya tuntubi lauyoyi don daukar mataki na gaba.

Idan ba a mantaba, a kwanakin baya tsohon gwamnan ya bukaci kotu da ta dakatar da EFCC kan binciken duk abinda ya shafi bidiyon dalar.

Kano: Rimingado Ya Sha Alwashin Sake Binciko Badakalar Ganduje Akan Dala

A wani labarin, Shugaban Yaki da Cin Hanci a Kano, Muhuyi Rimingado ya sha alwashin sake binciko bidiyon dala.

A wani faifan bidiyo an gano, tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje yana dura daloli a aljihunsa.

Rimingado wanda aka dawo da shi kujerar bisa umarnin kotu ya yi alkawarin kauda cin hanci a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel