Zamfara: Daliban Jami'ar Gusau Sun Balle da Zanga-Zanga, Sun Toshe Babban Titi
- Wasu dalibai sun tsunduma zanga-zangar lumana a Gusau, babban birnin jihar Zamfara ranar Asabar, 17 ga watan Yuni, 2023
- Ɗaliban waɗanda mafi akasarinsu suna karatu ne a jami'ar tarayya da ke Gusau sun fara zanga-zanga ne kan abokan karatunsu ɗalibai 5 da aka sace
- Rahoto ya nuna cewa masu zanga-zangar sun toshe babban titin Sakkwato zuwa Zariya wanda ya ratsa ta Gusau
Zamfara - Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka wasu ɗaliban sun tsunduma zanga-zanga a Gusau, babban birnin jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa ɗaliban sun ɓalle da wannan zanga-zanga ne kan abokan karatunsu ɗalibai 5 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Mafi akasarin masu zanga-zangar ɗalibai ne a jami'ar tarayya da ke Gusau kuma zuwa yanzu sun toshe babban Titin Sakkwato zuwa Zariya, wanda ya bi ta Gusau.
Da Dumi-Dumi: Mummunan Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Fasinjoji Da Dama a Wata Jiha, Rayuka Masu Yawa Sun Salwanta
Rahoton TVC News ya nuna cewa zanga-zangar ɗaliban jami'ar ya haddasa cunkoso a kan babban Titin, masu motocin haya da fasinjoji sun maƙale ba hanyar wucewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke fama da hare-haren yan bindigan jeji da masu garkuwa da mutane.
'Yan bindiga sun kashe kwararren Likita
A ranar Litinin da ta gabata, wasu 'yan bindiga suka yi ajalin kwararren Likita kuma suka yi awon gaba da mutane 10 ciki harda iyalansa a ƙauyen Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara.
Mazauna garin sun shaida cewa 'yan ta'addan sun shiga garin da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar dare kuma daga zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
Garin Jnagebe na ɗaya daga cikin yankuna da suke fama da hare-hare 'yan fashin daji a kai a kai. Daga watan Janairu, 2023 zuwa yau, mazauna sun ce aƙalla sau huɗu 'yan ta'adda suka kai musu hari.
Idan baku manta ba, a watan Fabrairu, 2021, mahara suka yi awon gaba da aƙalla ɗalibai mata 200 daga wata Sakandire a cikin garin Jangebe.
Ɗalibin jami'ar 'Federal University Gusau' ya shaida wa Legit.ng Hausa ta wayar tarho cewa tabbas sun yi zanga-zangar ne a garin Damɓa domin nuna fushi da yawan garkuwa da ɗalibai.
A cewarsa, abokan karatunsu na zama a gidajen ɗalibai masu zaman kansu a Damɓa, kuma yan bindiga suna musu ɗauki ɗai-ɗai, su zo su tafi da ɗaya, biyu wani lokacin 5.
Ɗalibin, wanda ya nemi a sakaya bayanansa saboda hali na tsaro, ya shaida wa wakilinmu cewa:
"Eh tabbas mun yi zanga-zanga duk da ban samu zuwa ba saboda a can Damɓa ne aka yi. Abokan karatunmu na zama a Damɓa, to 'yan bindiga mun matsa mana, su sace 1, 2 wani lokacin 5."
"Babu wani mataki da ake ɗauka shiyasa ɗaliban da ke zama a wurin suka gaji suka fito wannan zanga-zanga. Sai da aka turo motocin sojoji sannan ɗaliban da suka fita suka hakura."
Ya kara da cewa ɗalibai sun so ƙara fita zanga-zanga washe gari ranar Lahadi amma Sojoji suka hana su, yanzu haka dai an tura sojoji da yawa Damɓa.
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malamin Coci a Jihar Benuwai
A wani rahoton na daban Yan bindigan da ake zaton masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa ne sun yi awon gaba da Malamin Coci a jihar Benuwai.
Malamin Cocin da maharan suka yi garkuwa da shi yana aiki a St. Margaret’s Parish da ke garin Ajegbe Awume, ƙaramar hukumar Ohimini.
Asali: Legit.ng