"Ribas Ba Jihar Kirista Bane": Tsohon Shugaban Tsagerun Neja Delta Asari Dokubo Ya Gargadi Gwamna Fubara

"Ribas Ba Jihar Kirista Bane": Tsohon Shugaban Tsagerun Neja Delta Asari Dokubo Ya Gargadi Gwamna Fubara

  • Tsohon tsageran Neja Delta, Alhaji Asari Dokubo, ya soki iƙirarin da Gwamna Siminalayi Fubara ya yi na cewa jihar Ribas jihar Kiristoci ce
  • Dokubo ya caccaki gwamnan kan fara wa’adin sa bisa turbar da ba ta dace ba, sannan ya jaddada muhimmancin haɗin kai da kuma ‘yancin addini
  • Ya shawarci Gwamna Fubara da ya janye kalaman nasa, inda ya tabbatar da cewa jihar Ribas ba jihar Kiristoci ba ce kuma ba za ta taɓa zama ba

Rivers - Tsohon dan tsageran Neja Delta, Alhaji Asari Dokubo, ya yi nuna rashin jin daɗinsa kan kalaman da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya yi, na cewa Ribas jihar Kiristoci ce.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023, gwamnan ya bayyana cewa jihar za ta ci gaba da tsayuwa a kan daɓi'unta na Kiristanci.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Daga Hawa Mulki, Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata Daga Aiki

Asari Dokubo ya caccaki Gwamna Fubara kan kalaman da ya yi
"Ka janye kalamanka, jihar Ribas ba jihar Kiristoci ba ce," Asari ya fadawa Fubara. Hoto: Ripples Nigeria
Asali: UGC

Kalaman gwamnan sun saɓawa ƙa'idojin haɗin kai inji Asari Dokubo

Sai dai da yake mayar masa da martani a shafinsa na Facebook ta bidiyo na kai tsaye, Dokubo ya koka kan yadda Fubara ya fara wa'adin sa bisa turbar da ba ta dace ba, kamar yadda The Punch ta kawo rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada cewa yin irin wannan tsokaci ya saɓa wa ƙa'idojin haɗin kai da kuma 'yancin addini.

Dokubu ya nemi Gwamna Fubara ya janye kalamansa

Dokubo ya kuma ƙara da cewa gwamnan ba shi da hurumin ayyana jihar a matsayin jihar Kirista.

Ya ce jihar ta kowa da kowa ce ba ta wani addini guda daya ba, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

"Ina amfani da wannan kafar don bai wa gwamna shawara, Sim Fubara, akan ya janye kalaman da ya yi."
“Ina son ya sani cewa jihar Ribas ba jihar Kiristoci ba ce kuma ba za ta taɓa zama hakan ba. Da irin wannan kalaman, zan iya cewa gwamna ya fara mulki bisa kuskure,”.

Kara karanta wannan

Wike: Tsohon Gwamnan Ribas Ya Bayyana Dalilin Da Ya Kamata APC Ta Yi Godiya Ga Allah, Ya Kuma Caccaki PDP

Ga kalaman na Gwamna Fubara:

Wike ya musanta yin maguɗin zaɓe a jihar Ribas

A wani labarin na daban, tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya musanta zargin da jama'a suke na cewa ya yi maguɗin zaɓe wa Shugaba Tinubu a zaɓen da ya gabata.

Wike ya jaddada cewa shi fa bai yi wani maguɗin zaɓe domin wani ɗan takara ba, inda ya kuma ce yanzu batun na gaban kotu, kuma za ta bayyana gaskiyar cewa an yi maguɗin ko ba a yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel