Jan Aiki A Gaban Radda: Katsina Na Kashe N97m Da Litan Mai 127,000 Duk Wata Don Samar Da Ruwan Sha

Jan Aiki A Gaban Radda: Katsina Na Kashe N97m Da Litan Mai 127,000 Duk Wata Don Samar Da Ruwan Sha

  • Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana makudan kudade da ta ke kashewa duk wata don samar da ruwan sha a jihar
  • Sakataren din-din-din a ma'aikatar Ruwa ta jihar, Alhaji Rabo Danmusa shi ya bayyana haka yayin ganawa da 'yan jaridu
  • Rabo ya ce akalla litan bakin mai 127,000 suke samar wa a ko wane wata akan kudi N97m don samar da ruwa a fadin jihar

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa ta na kashe akalla N97m a ko wace wata don siyar litan bakin mai 127,000 don samar da ruwan sha a fadin jihar.

Sakataren din-din-din a ma'aikatar Ruwa ta jihar, Alhaji Rabo Danmusa shi ya bayyana haka yayin amsa tambayoyi daga 'yan jaridu a ofishinsa da ke Katsina.

Katsina na kashe N97m duk wata don samar da ruwa sha a jihar
Jihar Katsina Na Kashe N97m da Litan mai 127,000 Duk Wata. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa bakin mai din ana tura shi zuwa yankuna 10 da suka hada da Malumfashi da Funtua da Dutsimma da kuma Jibia, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Ga irinta nan: Yadda aka yiwa masu kwacen waya 2 a Kano hukunci mai tsanani a kotun Muslunci

Sauran bangarorin da ake samar da ruwan sha a jihar

Sauran sun hada da bangaren ruwa na Zobe da yankin ruwa na Kofar Kaura da Daura da Dutsi da Sabke da kuma Mashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tattaro cewa wadannan duka bangarorin ruwa ne da ke tura ruwa zuwa birnin Katsina da sauran yankunan da kewaye da su.

Danmusa ya kara da cewa gwamnatin jihar ta yi kokarin samar da ruwan har na tsawon shekaru takwas wanda ya kawo sauki ga a matsalar ruwa da ya addabi jihar.

Ya yabi sabuwar gwamnatin Radda bisa kokarin kawo sauki a harkar ruwan sha a jihar

Ya ce gwamnatin Dikko Radda ta riga ta fara kawo sauyi a harkar ruwan sha don gwamnatin tana samar da baikin mai da alimun da sauran dabaru don ci gaba da samar da ruwan ga al'umma.

Kara karanta wannan

Kashe-Kashen Zamfara: Sabon Gwamna Dauda Lawal Ya Daukarwa Zamfarawa Muhimmin Alkawari

Danmusa ya ce ziyarar da Gwamna Dikko Radda ya kai Dam din ruwa na Danja a farko mulkinsa ya nuna yadda ya matsu don ganin ya samar da ruwan wadatacce don noman rani da kuma amfanin al'umma.

Mazauna Garin Daura a Katsina Sun Roki ’Yan Najeriya Su Yafe Wa Buhari Kura-Kuransa

A wani labarin, wasu mazauna garin Daura da ke cikin jihar Katsina sun roki 'yan Najeriya da su yafe wa tsohon shugaban kasa Buhari.

Buhari ya mika mulki ne a ranar Litinin 29 ga watan Mayu ga sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel