Kashe-Kashe: Gwamna Lawal Ya Ba Da Tabbacin Tura Jami’an Tsaro Zuwa Kauyukan Zamfara

Kashe-Kashe: Gwamna Lawal Ya Ba Da Tabbacin Tura Jami’an Tsaro Zuwa Kauyukan Zamfara

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya magantu a kan sabon hare-haren da yan bindiga suka kai kan wasu garuruwan jihar
  • Gwamna Lawal ya sha alwashin tura jami'an tsaro zuwa kauyukan da abun ya shafa tare da basu kayan agaji
  • Tsagerun yan bindiga sun kai hare-hare kan kauyukan Janbako da Sakkida da ke karamar hukumar Maradun inda suka kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba

Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi alkawarin taimakawa iyalan wadanda aka kashe a hare-hare kan kauyukan Janbako da Sakkida da ke karamar hukumar Maradun ta jihar.

Lawal ya yi alkawarin ne lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya da jaje ga garuruwan da abun ya shafa.

Dauda Lawal, gwamnan jihar Zamfara
Kashe-Kashe: Gwamna Lawal Ya Ba Da Tabbacin Tura Jami’an Tsaro Zuwa Kauyukan Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Malam Mani Malam Mumini, ya ce gwamnatinsa na aiki tukuru don magance yawan hare-hare a jihar.

Ya kuma kara da cewar an tuntubi jami'an tsaro sannan za a tura karin jami'ai zuwa garuruwan, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce gwamnatin jihar na tsara hanyoyin da za a bi wajen taimaka wa marasa galihu da ma al’ummomin da suka yi fama da matsalar yan fashi da barayin shanu na tsawon shekaru.

Darakta Janar na labaran jihar, Malam Nuhu Salihu Anka, ya ce gwamnatin jihar na shirya jerin sunayen mutanen da miyagun kusa kashe don taimaka masu.

Anka ya ce:

"Gwamnatin ta bayar da gudunmawar naira miliyan 2 ga iyalan da abun ya shafa kuma jami'ai za su fara aiki nan ba da jimawa ba don ganin yawan barnar da maharan suka yi sannan su shirya tsari mai kyau na saukaka wahalar da mutanen ke ciki.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto da farko cewa Gwamna Lawal ya yi Allah wadai da hare-haren da yan bindiga suka kai kan garuruwan Sakiddar Magaji da Janbako a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Lawal ya yi Allah wadai da harin ne a cikin wata sanarwa da hadimin labaransa, Mustafa Jafaru-Kaura ya saki a Gusau.

Gwamna Lawal ya ba Matawalle wa'adin kwanaki 5 ya dawo da motocin gwamnatin Zamfara da ya sace

A wani labarin kuma, Dauda Lawal, sabon gwamnan jihar Zamfara, ya ba magabacinsa, Bello Matawalle wa'adin kwanaki biyar domin ya dawo da motocin gwamnati da jami'ansa suka yi awon gaba da su yayin da yake a matsayin gwamnan jihar.

Lawal, wanda ya kasance zababben gwamna karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayar da wa'adin ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya saki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel