Kotu Ta Dakatar da NLC da Wasu Kungiyoyi Daga Shiga Yajin Aiki

Kotu Ta Dakatar da NLC da Wasu Kungiyoyi Daga Shiga Yajin Aiki

  • Kotun ɗa'ar Ma'aikata a Abuja ta hana NLC da sauran kawayen ƙungiyar kwadago daga tsunduma yajin aiki ranar Laraba, 7 ga watan Yuni
  • Alkalin Kotun ya ɗauki wannan mataki ne yayin yanke hukunci kan bukatar da Ofishin AGF kuma ministan shari'a ya shigar
  • Ta ce ba zai yuwu ma'aikata su shiga yajin aiki yayin da daliban Sakandire ke zana jarabawar fita daga matakin Sakandire (WAEC) ba

FCT Abuja - Kotun ɗa'ar ma'aikata mai zama a Abuja ta dakatar da shirin tsunduma yajin aiki wanda ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) ke yi kan cire tallafin man fetur.

A ranar Litinin, 5 ga watan Yuni, 2023, Alkalin Kotun, mai shari'a Olufunke Anuwe, ya hana NLC da sauran ƙungiyoyin kwadugo shiga yajin aikin da suka tsara.

Tutar NLC.
Kotu Ta Dakatar da NLC da Wasu Kungiyoyi Daga Shiga Yajin Aiki Hoto: NLC
Asali: Twitter

Alkalin ya haramtawa dukkan ƙungiyoyin tafiya yajin aiki daga ranar 7 ga watan Yuni, har sai Kotun ta yanke hukuncin karshe kan karar da aka shigar gabanta, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin Kungiyoyin Ma’aikata 8 da Za Su Shiga Gagarumin Yajin-Aikin Da NLC Za Ta Shirya

Haka nan kuma Kotun ta umarci NLC ta gurfana a gabanta kamar yadda takardar sammaci ta isa ga ƙungiyar a ranar da za'a ci gaba da zaman shari'ar, 19 ga watan Yuni.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne kan buƙatar cikin shari'a da Ofishin Antoni Janar na ƙasa (AGF) kuma Ministan shari'a ya nemi dakatar da shirin shiga yajin aikin.

Meyasa Ƙotu ta hana shiga yajin aikin?

Da take bayanin dalilin hana shiga yajin aikin, Kotu ta ce bai dace ƙungiyoyin kwadaho su shiga yajin aiki a halin yanzu ba saboda ɗalibai sun faɗa zana jarabawar fita daga Sakandire (WASSCE).

A jadawalin WAEC, jarabawar ɗalibai ta wannan shekara 2023 ta fara ne daga ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2023da muke ciki, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Dalilai 5 Da Yasa Yajin Aikin NLC Kan Man Fetur Ba Zai Yi Nasara Ba

Gwamnatin Tinubu Ta Kara Shiga Sabon Zama da 'Yan Kadugo a Abuja

A wani rahoton na daban kuma Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da zaman tattaunawa da ƙungiyoyin kwadugo kan cire tallafin man fetur.

Taron wanda ya tashi ba tare da fahimtar juna ba ranar Lahadi, 4 ga watan Mayu, 2023, ana tsammanin cimma matsaya a zaman yau Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262