An Samu Cikas, Kyaftin Ya Fadawa Gwamnati Jirgin ‘Nigeria Air’ Ba Zai Fara Aiki ba

An Samu Cikas, Kyaftin Ya Fadawa Gwamnati Jirgin ‘Nigeria Air’ Ba Zai Fara Aiki ba

  • Da kamar wahala jirgin saman Nigeria Air da aka shigo da shi a kurarren lokaci ya iya fara tashi
  • Kyaftin Ado Sanusi ya ce ana bukatar a bi wasu matakai kafin jirgin ya fara tashi da fasinjoji tukuna
  • Shugaban kamfanin na Aero Contractors ya ce sai hukumar NCAA ta bada izini sannan jirgi zai daga

Abuja - Shugaban kamfanin Aero Contractors Ado Sanusi ya yi magana a game da shirin gwamnatin tarayya na kafa kamfanin jirgi na kasa.

A ranar Juma’a Daily Trust ta rahoto Kyaftin Ado Sanusi ya na cewa kawo jirgin Nigeria Air da aka yi bai nufin jirgin saman zai fara jigila nan take.

Kyaftin din ya yi magana ne a matsayinsa na kwararren masanin harkokin jiragen sama.

Nigeria Air
Jirgin Nigeria Air Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Da aka zanta da shi a tashar Channels dazu, Sanusi ya ce kawo jirgi cikin Najeriya dabam, sannan jirgin ya samu damar fara kasuwanci kuma dabam.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba Za Mu Daina Bada Kwangiloli da Cin Bashi ba Sai Daren 29 ga Watan Mayu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar masanin jiragen, ba za ta yiwu kamfanin jirgi ya soma daukar fasinja kwana biyu da shigo da shi ba, ya ce akwai wasu matakai da ake bi tukun.

Duniya ta na kallo, Kyaftin Sanusi ya na ganin da kamar wahala hukumar NCAA ta yi watsi da sharudan da ta gindaya kafin a fara yin amfani da jirgin.

Abin da Ado Sanusi ya fada

Kafin a bada dama jirgi ya samu lasisin AOC, Sanusi ya ce sai ya yi tashi na gwaji an tabbatar da ya na da lafiyar yin yawo a sararin samaniya.
Saboda haka ba zai yiwu ba kurum jirgin ya fara tashi nan da kwanaki biyu. Ba za ta yiwu ba.
Saboda ba su yi tashin gwaji ba, dole ayi tashi biyar, kasashen Dunya su na kallonmu domin ganin ko mu na bin sharudan ICAO da ya yanke matakan da ake bi wajen fara daukar fasinjoji a kasashen ketare

Kara karanta wannan

Wuta Ta Kona Gidan da Ganduje Zai Zauna Bayan Ya Bar Fadar Gwamnatin Kano

A dalilin haka ba na tunanin Darekta Janar da ya yi aiki a ICAO a baya zai yi watsi da dokokin nan.
Saboda haka kawo jirgin sama dabam sannan kuma wani abu ne dabam ya fara daukar fasinjoji.

- Ado Sanusi

Ayyukan wuta a Daura

Rahoto ya zo Gwamnatin tarayya ta ba kamfanin Power Deal Construction Ltd kwangilar lantarki a Daura a karshen mulkin Muhammadu Buhari.

Kamar yadda Ministan harkokin lantarki ya fada, wannan aiki da zai ci N4bn zai dauki ‘dan lokaci, an kuma bada wasu kwangilolin a Yobe da Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel