Saura Kwanaki 6 a Bar Aso Rock, Hanan Tayi Magana a Kan Mulkin Shugaba Buhari

Saura Kwanaki 6 a Bar Aso Rock, Hanan Tayi Magana a Kan Mulkin Shugaba Buhari

  • Hanan Muhammadu Buhari ta wallafa hoton Mai girma Shugaban Najeriya, ta kwarara masa yabo
  • ‘Diyar shugaban kasar mai jiran gado ta ce a boye Mahaifinta ya rika samun nasarori a gwamnatinsa
  • A ‘yan kwanakin nan, Buhari ya na yawon kaddamar da manyan ayyukan da gwamnatinsa ta yi a kasa

Abuja - Hanan Muhammadu Buhari ta na cikin ‘ya ‘yan shugaban Najeriya mai barin gado, an ji ta ta na yabon mahaifin na su.

Da ta ke magana a shafin Instagram a ranar Talata, 23 ga watan Mayu 2023, Hanan Buhari ta jinjinawa kokarin shugaban kasa.

Daily Trust ta ce wannan Baiwar Allah ta wallafa hoton mahaifinta ya na kaddamar da jiragen ruwan yaki a Legas a makon nan.

Buhari
Muhammadu Buhari a kan teku Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

A hoton sai Hanan ta rubuta:

Kara karanta wannan

Buhari Ya Sake Yin Nadin Sababbin Mukamai Ana Saura Kwana 6 a Rantsar da Tinubu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mahaifi na…Wanda ya samu nasara a boye!” - Hanan Buhari

Ayyukan gwamnatin Buhari

Babu mamaki yadda shugaban kasar yake yawon kaddamar da ayyuka ne Hanan ta ke ganin mahaifinsu ya cancanci a yaba masa.

A ranar Talata, Mai girma Muhammadu Buhari ya kaddamar da Hedikwatar hukumar kwastam wanda aka gina a kan kusan N20bn.

Haka zalika gwamnatin tarayya ta gama aikin gadar Neja bayan tsawon shekara da shekaru, sannan an bude matatar man Aliko Dangote.

Hanan a Instagram

Hanan mai ‘ya daya a Duniya ta na auren Muhammad Turad, daya daga cikin Hadiman Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola.

Legit.ng Hausa ta fahimci ‘yar shugaban kasar ta na da mabiya fiye da 143, 000 a dandalin Instagram, ta na kuma bibiyar mutane 450.

Rabon da Hanan Muhammadu Buhari ta daura hoto a shafinta tun a farkon shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Minista Ya Cigaba da Korar Shugabannin Hukumomi, Ya Ce Babu Sani ko Sabo a Mulki

Babatun Gwamnan Kano

A wani faifai da aka fito da shi, an ji labari Abdullahi Ganduje bai ji dadin yadda Bola Tinubu ya zauna da Rabiu Kwankwaso a Faransa ba.

Gwamnan ya na magana ne ga wani da ake zargin Ibrahim Kabir Masari ne, ya ke cewa za ayi watsi da su saboda za su bar gadon mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel